HALAYEN DA YA KAMATA MIJI YA GUJEWA SADUWA DA MATARSA A CIKIN SU


*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI* 

*_HALAYEN DA YA KAMATA MIJI YA GUJI SADUWA DA MATANSA_*

Ya kamata miji ya san cewa akwai wadansu halayen da idan namiji ya samu kansa a cikinsu bai kamata ya sadu da iyallinsa a ciki wadannan halayen ba, yana cutar da dan adam, kamar yadda malamai masana saduwa suka bayyana, halayan kuwa sune kamar haka; 

1. Saduwa yayin da mutum yake jin yunwa.

2. Saduwa lokacin da mutum ya koshi da yawa.

3. Saduwa yayin fushi.

4. Saduwa lokacin bakin ciki.

5. Saduwa yayin tsananin farin ciki

6. Saduwa bayan fitowa daga bandaki.

7. Saduwa lokacin da matan ke cikin rashin lafiya.

8. Saduwa yayin fargaba.

Da dai sauransu domin yana raunata gabobin jikin dan adam, amma kuma ba laifi ba ne don mutum ya sadu da iyalinsa a kowane lokaci matukar dai matan na cikin tsarki. Kuma bai je mata ta inda ya haramta ba.

Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*
Post a Comment (0)