HANYAR SAMUN YARO NAGARI 1


👳🏻‍♀️ *HANYAR SAMUN YARO NA GARI 01* 🧕🏻

Gabatarwa: Bismillahi Rahmanirraheem. Yabo da jinjina sun tabbata ga Allah S.W.T, Allah ya yi salati da Taslimi ga Annabi S.A.W da iyalansa da sahabbansa sa wanda suka bisu da kyautatawa.
Bayan haka: Wannan littafi ne da muke gabatar dashi mai taken HANYAR SAMUN YARO NA GARI wanda shi ne burin duk wani uba a dorin qasa. Kuma shi ne wanda Allah ya fadama mala'iku cewa zai sanya shi a matsayin khalifah a doron kasa. Muna fatan Allah ya mana jagora yasa ya amfanemu daku baki daya.

📜 *ABUBUWAN DAYA KUSA*📜

⏹️ Gabatarwa

1. Tarbiyyar kafin ayi aure
▪️Zamantowar uwa ko uba na kirki
▪️Zaben uwa ko uba ba qwarai
▪️Bin dokokin shari'ah wajen neman aure
▪️Daura aure na shari'ah
2. Tarbiyar bayan daura aure
▪️Adduah ga ango da amarya
▪️Tausasama amarya daren farko
▪️Yima amarya adduah ▪️Sallah da amarya
▪️Adduah lokacin saduwa
▪️Walima ta Shariah
▪️Adduar samun yaro na gari

3. Tarbiyyar bayan daukan cikinsa zuwa lokacin haihuwa
▪️Godiya gameda samun ciki
▪️Yarda duk abinda Allah ya bayar
▪️Yima yaro adduah da zarar an haifeshi
▪️Yima yaro Tahneeki
▪️Zabama yaro suna mai kyau
▪️Yanka (Aqeeqa) ga yaro

4. Tarbiyyar shekaru (1-7)
▪️ Cikakkiyar shayarwa
▪️ Mai aiki ta qwarai
▪️Koya ma yaro Kalmar tauheedi
▪️Tsarkake gida daga kayan wasanni da kade-kade
▪️Tsare gida da Qur'ani, da zikiri da salloli

5. Tarbiyyar shekaru (7-14)

▪️Karantar dashi Qur'ani
▪️Umurtar yara da Sallah
▪️ Raba ma yara wajen kwana
▪️ koya ma yaro da'a
▪️ Zabo ma yara makaranta
▪️ Malamin kirki da abokai na qwarai
▪️Dasa ma yara son Malamai da shuwagabanni da musu biyayyah
▪️Tufafin da suka dace

6. Tarbiyyar Shekara (14-21)

▪️Karantar dashi Addini
▪️Sauran ladubba na kirki
▪️Jawosu a jika da shawara dasu
▪️ Ilimin Zamani
7. Tarbiyyar shekaru(21- sama)
▪️Yima yara aure
▪️Bibiyar yara bayan aure
▪️Sanyasu jagoranci a wasu abubuwa
▪️Yima yara wasiyya kafin mutuwa

⏹️ Kammalawa.


Muna fatan Allah yasa ma rubutun albarka ya zama dalilin gyara wasu kura kurai da mukeyi kuma yasa hanyace da za a cigaba da samun yara na gari.





Abu Isma'il 
Markazul Wa'ayil Islamiy
Ramadan Daura
2/8/1441- 25/4/2020.
Post a Comment (0)