MAGANIN SANYIN GAƁOƁIN JIKI


MAGANIN SANYIN GABOBIN JIKI (ARTHRITIS.

 ALBASA DA MAN HABBA.


Barkan mu da sake saduwa.A yau kuma munyi dubane zuwa ga wasu sakonnin da muke samu a wasu lokuta daga masu bibiyar wannan shafin kan abinda ya shafi sanyin ga6o6in jiki waton (arthritis) a turance.

Dukda yake akoi magunna da dama da ake amfani da su wajen maganin sanyin kashi sai dai kuma mukan dubi masu saukin nema da hadawa ga masu bukata.

Sanyin kashi ba sanyi bane Wanda ake dauka ta saduwa waton (sexually transmitted diseases) a dan haka baya da wata alaqa da wannan. Wasu dai yakan zo mu sune ba zata,ba tareda sanin ainihin dalilin ciwon ba,wasu kuma yana da alaqa da irin ayukkan da suke yi na yawan ta'ammali da ruwa akai akai ko kuma wurare masu dausayin sanyi,wasu a sanadin kwankwadar wasu rukunnan kwayoyin bature ne da makamantansu.

Zaka tarar wani sashe na gangar jiki ko wata ga6a a jiki na ciwo yala guiwa ce ta kafa,guiwar hannu,qobro,kafada ce,kashin baya,a bayan wuya da sauransu.

Anan za a nemi albasa qatuwa sai a nemi man habba a yayyanka albasar a soya da man habba sai albasar ta qone,sai a nemi man kade a gauraya a kan tafin hannu yan da kasan idan za'a shafa man shafi na jiki(Vaseline) to sai a gasa wajen da ruwan zafi masu dumi,sai wurin yayi laushi sosai,za a nemi kyalle mai haske a rinka tsomawa a cikin ruwan zafi ana diba ana dannawa a inda ke ciwon ,daga bisani sai a dibi wannan mai na albasa da habba a gauraya da mankade sai a shafa.
Idan ba mankade a shafa a haka.
A zanka yin haka a sanda ake bukata musamman idan an tashi bacci da safe da kuma lokacin da za a shiga bacci.
Za a samu sauki sosai da amincewar Allah.
Idan har wannan maganin bai amshe kaba to ka kira ni kai tsaye mu tattauna da kai naji yanayin matsalar da jimawarta a jikinka.Domin wani kusan a kullum yana tareda wannan matsalar gaya kuma shan kwayoyin bature na sanyin qashi na haddasa wasu matsaloli masu lahani a jiki.

08066682273 08025713807
Post a Comment (0)