HIJABIN MACE MUSULMA DA NIQAB 2


Fotowa ta (2)

📚DAGA ZAUREN HADISAN ANNABI📚

*HIJABIN MACE MUSULMA DA NIQABI*


 *ASSALAMU'ALAIKUM* 

Dukkan godiya ta tabbata ga ubangiji Wanda ya sanya mana tufafi dan yazama kariya da ado ga dan Adam 
 Salati da daukaka su tabbata ga annabinmu da alayen gidansa da sahabbansa baki daya. 


A karshen rubutumu na (1)munyi alkawarin zamu kawomuku ma'anar wannan ayar da take cikin سورة الأحزاب  

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

يايهاالنبى قل لازوخك وبناتك ونساء المؤمنين يدنين علهن من خلبيبهن ذلك ادنى ان يعرفن فلايؤذين وكان الله غفورارحيما ٠:٠
*YA WANNAN ANNABI KA FADAWA MATANKA DA "YA"YANKA DA SAURAN MATAN MUMINAI DA SU DINGA SAUKAR DA JULBABINSU WANNAN SHINE YAFI KUSANTAR,DASU DA A GANE SU NA KWARAINE KUMA KA DA CUTARDASU LALLAI ALLAH MAI GAFARANE MAI JIN KAI*


Yaku alummar musulmi a wannan ayar da Allah ya saukarwa annabinsa Allah yana umartar mata da lullube jikinsu gaba daya Dan haka wannan umarni da Allah yayiwa mata to umarnine na wajibi Amma abin takaicin shine yadda mata a yau suke yin shigar jahiliyyar farko bayan Allah yaja hankalin mata a wata aya da kada su dainga fita irin ta jahiliyyar farko 

Nasan Mai karatu zai yadda Dani idan nace Allah yayi mana umarni da mu dinga tsayar da sallah a Qur'ani nasan kowa yasan sallah wajibice ta yadda duk Wanda ya baya sallah to za'ayimasa wani gani-gani to dede take da wacce tace bazata saka hijabiba dan duk umarnin Allah ne .

 Haka *shekul islam ibn temiyya*
Yana cewa a littafinsa *maj'mu'ul fatawa mujalladi na 28 shafi na 210 zuwa na 211* Yana cewa Amma julbabi shine abinda zai rufe tundaga fiska har zuwa kasa Dan haka hada HIJABI da NIQABI guri daya shine julbabin da Allah yake nufi 

Hadisi yazo a muwadda Malik da ummu salama matar annabi s,a,w ta tambayeshi cewa munasaka hijabi har Yana jan kasa shi akwai bukatar mu dinga dagawa sai yayimata umarni dama su dinga barin shibiri daya Yana jan kasa domin idan najasa ta sameshi to kasar da ke biyo baya tana gogeshi .



Ya "yan,uwa musulmi musani duk abu me daraja boyeshi ake dan haka idan har fito da tsiraici wayewace to lallai dabbobi sunfi me baiyyana jikinta a waje ga wadanda basu hallata su gani ba to sunfita wayewa.



Insha Allah a rubutu na gaba zamuji wadanne suffofi hijabi zai cika har ya zama cikakken hijabi  

*Allah yasa mu dace*



*Ummu Ahmad✍🏻*
Post a Comment (0)