Fotowa ta (1)
📚DAGA ZAUREN HADISAN ANNABI📚
*HIJABIN MACE MUSULMA DA NIQABI*
*ASSALAMU'ALAIKUM*
Dukkan godiya ta tabbata ga ubangiji Wanda ya sanya mana tufafi dan yazama kariya da ado ga dan Adam
Salati da daukaka su tabbata ga annabinmu da alayen gidansa da sahabbansa baki daya.
يايهاالنبى قل لازوخك وبناتك ونساء المؤمنين يدنين علهن من خلبيبهن ذلك ادنى ان يعرفن فلايؤذين وكان الله غفورارحيما ٠:٠
Wannan itace ayar da Allah madaukakin sarki ya saukarwa da annabinmu akan hukuncin lullube jiki da julbabi saboda hikimomi masu tarin yawa daga cikinsu zamu kawo kadan daga ciki
🕸 Hikima ta farko Allah madaukakin sarki yana kishinmu shiyasa ya sanya mu mata mu dinga rufe jikinmu domin mace tanada daraja da mutunci da kima kuma duk abu me daraja boyeshi ake .
☘Hikima ta biyu dan mu ware da jinsi ko kamance ceniya da dabbobi tunda su haka suke fitowa ba kaya dan haka idan har fito da tsiraici wayewace to lallai dabbobi sunfi me baiyyana jikinta a waje ga wadanda basu hallata su gani ba to sunfita wayewa.
Insha Allah a rubutu na gaba zamu kawomuku ma'anar wannan ayar tarda sauran hikimomi akan saka hijabi
*Allah yasa mu dace*
