RUFE MASALLATAI DOMIN GUDUN YAƊUWAR CORONAVIRUS 2


RUFE MASALLATAI DOMIN GUDUN YAƊUWAR CORONA VIRUS, HAKAN YA SAƁAWA SUNNAR ALLAH DA MANZON ALLAH (S.A.W) 


               0️⃣0️⃣2️⃣

Allah Yace a Lahira Kuma inada Azaba Mai Raɗaɗi. Abin Mamaki ne ma Wai Malami Ya Bada Fatawar Cewa Wai Babu Laifi Gwannati tasa a Kulle Masallatai. Wannan Wanne Irin ilmi ne? Ilmin da Za'a Kulle Wajen Yin Ɓautar Allah da Zikirin Allah.
       Akwai Wani Magana da Umar (RA) Yayi, Yace Babu Abinda Zai Gyara Karshen Al'umman Annabi Muhammad Mai Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata Agare Shi, Sai fa Abinda Ya Gyara Farkon Al'umman Manzon Allah. Kenan Mu Wannan Al'umman Babu Wani Abinda Zai Gyara Mana Al'amuran Mu Har Sai Mun Yi Koyi da Waɗancan Magabatan. 

Ace Wai An Kulle Masallatai Na Wani Jiha Ɗaya Tak, Don Allah Ka Suranta Ɓayin Allah Mutum Dubu Nawa Ka Hana Su Yin Sujada ma Ubangijin Su? Idan an Ce Kowa Ya Koma Ɗaki Yayi Sallar Shi a Cikin Ɗaki, Wanda Annabi Muhammad Mai Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata Agare Shi, Yana Cewa Kuyi Riko da Sunnata, Kuyi Riko da Sunnar Halifofi na Masu Shiryawa Kuma Shiryayyu. 
       Wannan Hadisin Manzon Allah Yace Mu Rika Duba Sunnar Sa da Sunnar Halifofin Sa Irin Su Aliyu, Usman, Umar Abubakar, Allah Ya Kara Yarda Gare Su. Yace Mu Duɓe Su Muyi Koyi da Su. 

Sai Annabi Yace Mana Ku Kiyaye Wasu Al'amura da Za'a Kirkiro Su, Yace Ku Kiyaye Duk Wani Abinda Za'a Kirkiro Su a Bayan Ƙasa. Duba Cikin Sunanul Abu Dawud, Yana Cikin Kitabul Sunnah Babul Uzuhul Sunnah, da Sunanul Tirmizy) 
       Kenan idan Annabi Muhammad Mai Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata Agare Shi, Zai Ce Muyi Riko da Sunnar Sa, Kenan Idan Wani ANNOBA Ya Same Mu ko Wani Masifa ya Auku Sai Mu Waiwaya Mu Dubi Magabatan Mu, Shin Irin Wannan Abun Ya Taɓa Aukuwa a Zamanin Su? Shin Me Suka Faɗa a Lokacin da Abin Ya Auku? Matukar Anyi Haka Zamu Samu Tsira a Wajen Allah____

Mu Hadu a Rubutu Na Gaba In Allah Ya Kaimu Lafiya. 

Daga Zauren Muslim Women Mata Zallah Whatsapp Group. 


MUHAMMAD TUKUR JALINGO 
Domin Shiga Wannan Group Ki Turo Mana Da Cikakken Sallama Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Kai Tsaye Ta Whatsapp Number Namu Kamar Haka 
(08164223447) Ko (08151796429) 
This Group Is Only For Women Please.
Post a Comment (0)