#SUNNANE GAGGAUTA BUDE BAKI
Ya dan uwa mai Azumi kasani lallai gaggauta buda baki yana cikin sunnar Manzon Allah s.a.w mai karfi,Manzon Allah yayi hakan a aikace kuma ya koyar tare da umarni da kwadaitarwa akan hakan.
Manzon Allah ﷺ yana cewa:
*(Mutane baza gushe ba suna cikin alkhairi mutuqar suna gaggauta bude baki)*
@ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﺡ 1856ﻣﺴﻠﻢ ﺡ 1098 ]
ﺍﺑﻦ ﻋﺜﻴﻤﻴﻦ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ.
Yana cewa:
*”Da wannan hadisin ne muke fahimtar lallai wadanda suke jinkirta bude baki har sai dare yayi tauraro yafito kamar yan shi’a Rafidha,basu kan alkhairin da Manzon Allah yake kansa,domin sun saba da koyarwarsa…”*
Kuma Manzon Allah ﷺ yana cewa:
*(Addinin Allah bazai gushe ba yana mai rinjaye akan sauran addinai mutukar mutune suna gaggauta buda baki,domin Yahudawa da nasara suna jinkirta buda baki)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ﺡ 2353
Daga Malik bn Anar yana cewa:Na shiga wajan uwar Masu Imani A’isha R.A ni da Masruq,sai nace:
“Ya Uwar masu Imani mutane guda biyu daga cikin Sahabban Manzon Allah ﷺ, daya daga cikinsu yana gaggauta buda baki yana gaggauta sallah,dayan kuma yana jinkirta buda baki yana jinkirta sallah,”sai tace waninene yake gaggauta bude baki yake gaggauta sallah?? Sai nace:
“Abdillahi bn Mas’ud R.A” sai tace:
*”Hakanan Manzon Allah ﷺ yake gaggauta buda baki kuma yake gaggauta sallah”*
@ﻣﺴﻠﻢ ﺡ 1099
*MAS’ALA*
Wanda yayi tsammani bisa yaqininsa cewa Rana ta fadi,sai yayi bude baki,daga baya sai ta bayyana cewa rana bata fadi ba,to yakame har zuwa faduwar ranar na zahiri kuma Azuminsa yana nan.
Saboda fadin Manzon Allah ﷺ
*(Lallai Allah yayi min rangwame akan al’ummata,akan abinda suka aikata abisa Mantuwa da wanda suka aikata abisa kuskure……)*
@ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ
Allah ne mafi sani.