KAR KAYI ASARAN LOKACINKA, TSAYA KA MORESHI.
Shaikh Ibnu Uthaimeen Allah ya masa rahama yana cewa "Ka ribaci lokacinka,ka sanya ma kanka wani abu na daga littafin Allah da zakana karantawa, ka sanya ma kanka lokaci na aikata ayyukan alkhairi, ka tashi cikin karshen Dare koda minti talatinne kafin fitowar alfjr, ka gana da Ubangijinka, ka rokeshi domin shi yana saukowa zuwa saman duniya yana cewa : (Waye zai rokeni in amsa masa, waye zai tambayeni in bashi, waye zai nemi gafarana in gafarta masa)".
شرح الكافية الشافية ٤/٣٨٠
# Zaurenfisabilillah
https://t.me/Fisabilillaaah
