KUN SAN ME YA SA ILIMI YA FI KUƊI?


KO KUNSAN ME YASA ILIMI YAFI KUDI?

IMAM ALIY (AS) YA BADA AMSA

An ta6a tambayar Imam Aliy (as) shin me yafi? Dukiya ko Ilimi?

Saiyace neman ilimi, yafi tara makuddan kudi, na dukiya, Sau (10).

1. Ilimi shine Gadon Annabawa, Kudi kuma Gadon Fir'auna, ne. A haka ilimi yafi kudi.

2. Dole ka tsare dukiyarka, amma iliminka zai tsareka.

3. Dukiya na jawo Maqiya amma ilimi na jawo Abokan amana da arziki.

4. Ilimi yafi kudi, don yana Qaruwa, a lokacin da ake badashi, amma kudi kan Ragu, da zarar an Fidda wani abu daga cikinsa.

5. Ilimi yafi, saboda Malamai kan badashi Kyauta, amma Attajirai kan zamo, Marowata sannan ga Kwadayin jibge dukiya.

6. Ilimi yafi, don baza'a iya Sace maka ilimi ba amma za'a iya, Sace dukiya, ka Tsiyace, amma ba'a zama jahili bayan anyi ilimi.

7. Ilimi baya Ru6ewa ko yaushe yananan, amma kudi, ko dukiya kanyi, Tsatsa bayan wani lokaci. Qarin ilimi na haifar da Basira, kuma yana dadewa yana qara Kima, amma kudi kan rage Daraja.

8. Ilimi yafi, don ilimi bayada Iyaka, amma dukiya nada Iyaka.

9. Ilimi na karfafa kwakwalwa , amma kudi kan 6ata tarbiyyar mutane.

10. Ilimi yafi, don yakan Qarfafa bauta, amma kudi kansa, Shagala

Allah ya ba mu ilimi mai amfani

*Khalifa Jega.*
*08060848930*
Post a Comment (0)