MU TUNA DA 'YAN UWANMU MABUƘATA


#Ramadhan

MU TUNA DA ƳAN UWANMU MABUƘATA

A yayin da muke ta shirye shiryen Sallah, ɗinke ɗinken sabbin tufafi, sayen sabbin takalma da jaka, ɗan kunne, sarƙa da kayan ado, hijabai da mayafai da dai sauransu ma kanmu da ƴaƴanmu, TO KAR MU MANTA DA ƳAN UWANMU DA BA SU DA HALIN YIN HAKAN.

Idan da hali su ma a sama masu wanda za su saka suyi fes fes ranar Idi kamar yanda kowa ya ke son kasancewa, idan sababbi ba su samu ba Uwar gida a duba musu cikin waɗanda a ke dasu a gida, a wanke a goge a feshesu da turare a aika musu, haka kai ma Mai gida a duba a cire wa mabuƙata su ma suyi farin ciki, cikin suturun yara ki duba ma wasu mabuƙatan ko marayu da ba su da mai yi musu in ma babu ikon sama musu sababbin.

Haka ku ma ƴan mata da samari, wasu sun tara kaya kamar suyi magana, amma ga sa'anninsu nan wasu ma abokansu ne a na tare amma kun barsu cikin tsimmokara!! 

Abin da yake tsoho a gurinka/ki to wani a gurinsa sabone tas.

Madallah da wanda ya shigar da farin ciki zuciyar dan uwansa.

Telegram:
https://t.me/ansarussunnah
Post a Comment (0)