#LOKUTA GUDA 5 MAFI TSADA A WATAN RAMADHANA:
Hakika lokacin watan Ramadhana lokaci ne mafi tsada gaba dayansa,amma akwai lokacuta mafi tsada cikinsu,wanda sunfi tsada a dukkan sauran lokuta baki daya.
1-Lokaci na Farko
*”Lokacin Shan Sahur”*
Wato daga da fitowar alfijir,wannan lokacin yana da albarka guda ukku:-
-Lokacin mai albarkane,
-Abincin sahur din mai albarkane
-sannan lokacine na amsa addua.
■Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Allah ya sanya albarka acikin abubuwa guda ukku,acikin jama’a da Sahur……)*
@Dhabarany
■Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Lallai Allah ya sanya albarka acikin Sahur da Awo)*
@Jami’i Sagheer
2-Lokaci na Biyu
*”Lokacin Bude baki*
Lokacin mai albarka guda ukku
-Lokacine na amsa addua
-Lokacin ne na farin cikin masu azumi lokacin buda bakinsu
-Lokacine na samun cin nasarar musulmai idan suna gaggauta buda baki.
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Mutane guda ukku ba’a mayar da addu’o’insu,adduar mai Azumi lokacin bude baki,da adduar Shugaba adali da adduar wanda aka zalumta)*
@Tirmzy da Bn Majah da ibn Hibban
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Mai Azumi yana da addua karbabbiya lokacin bude bakinsa)*
@Ibn Majah
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Addinin Allah bazai gushe ba yana mai samun rinjaye matuqar suna gaggauta bude baki)*
@Abu Dauda.
3-Lokaci na Ukku
*”Daren lailatul Qadri*
Lokacin mai albarka guda ukku
-Samun gafarar zunubai
-Lokacin na amsa addua
-Lokacin na rubanya ladar ibada
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Duk wanda ya raya daren lailatul Qadri, yana mai Imani yana mai neman Lada,an gafarta masa abinda ya gabatar na zunubansa)*
@Bukhari da Muslim
Mafi tsadar Abinda ake su karokin Allah shine,afuwa da gafara sannan karoki abinda kake so bayan haka,kamar yadda Hadisin Nana A’sha R.A ta tabbatar daga Manzon Allah s.a.w
4-Lokaci na Hudu
*”Lokacin da dare ya raba tsakiya,ko ya kai kashi ukku na karshe”*
Manzon Allah ِï·º yana cewa:
*(Idan dare ya wuce tsakiya,Ubangiji Tabaraka wata’ala yana saukowa zuwa samar duniya,sai ya riqa cewa:”Shin akwai mai rokona na bashi,Shin akwai mai wata buqata abiya masa,shin akwai mai neman gafara a gafarta masa,yana ta fadar hakan har zuwa fitowar alfijir)*
@صØÙŠØ Ù…Ø³Ù„ :(758)
5-Lokaci na biyar
*”Bayan sallar Assuba zuwa fitowar rana”*
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(…..Wanda ya zauna yana ambaton Allah bayan sallar assuba yana zaune a inda yayi sallah,yana ambaton Allah,har rana ta fito,sannan ya tashi yayi sallar raka’a biyu,bayan fitowar rana,za’a rubuta masa ladar Aikin hajji cikakkiya…)*
@Saheehul jami’i
Allah ne mafi sani.
Yan uwana muyi kokari wajan kula da murar wadan nan lokuta masu albarka.
Allah ka gafarta mini ni da mahaifana da sauran musulman duniya baki daya