MATSAYIN ZAKKA A SHARI'ANCE 16


_*⚖️MATSAYIN ZAKKA A' SHARI'ANCE⚖️*_()

ZAKKAR KAYAN SAYARWA :

 Abin da ake nufi da kayan sayarwa a nan,
 su ne kayan cinikin yau-da-kullum. 
Watau wadanda ake cinikin yau-da-kullum da su.

Shin a kanti aka zuba kayan, 
ko a rumfar kasuwa, ko kuma yawo ake yi da su.

 Dalilin wajabcin Zakkar kayan sayarwa ya bayyana a AlKur’ani da
 Sunnah da Ijma’i. Allah (SWT) Ya ce:

*"يأيها الذين ءامنوا أنفقوا من طيبات ما كسبتم، ومما أخرجنا لكم من الأرض..."*

“Ya ku wadan da suka yi imani ku bayar daga tsarkakan abin da kuka noma, haka nan daga abin da muka fitar muku daga Kasa”
(Al-baKara: 267.)

 A Sunna, kuma akwai hadisi da Abu Dawuda ya rawaito kamar haka:

*"عم سمرة بن جندب قال: كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يأمرنا أن نخرج الصدقات مما نعد للبيع"*

“Daga Samurata dan Jundubu ya ce: Manzon Allah (SAW) ya kasance yana umartar mu da mu dinga fitar da Zakka daga abin da muka tanada don ciniki”
(Abu Dawuda ya rawaito.).

 Dangane da ijma’i kuwa, 
sahabbai da sauran magabata sun hadu a kan fitar da Zakka ga kayan sayarwa.

 Nisabinsu:
Su kayan sayarwa ana la’akari da nisabinsu ne a sanda suka shekara,
kamar yadda Imamu Malik da Imamus Shafi’i suka ce. Watau jarin da ka fara ciniki da shi. Sai aka ga ya shekara da cika nisabi. Sai a fitar masa da Zakka.

 Yadda za a fitar da Zakkar shi ne,
dan kasuwa zai yi lissafin kayansa a Kimarsu ta saye ta wannan lokacin,
sai ya hada da bashin da yake zaton za a biya shi,
tare da abin da yake hannunsa,
sai ya kasa arba’in ya fitar da daya.

A sanda zai yi Kimar zai hada da kayan da ya bar su sai sun yi tsada.
Watau a kowace shekara zai fitar masa da zakka. Wannan shi ne abin da malamai suka ce, in ban da Imam Malik.

Shi a wajensa kayan da aka bari sai sun yi tsada, sau daya za a fitar musu da Zakka. (Duba FiKhuz Zakat juz’i na 1, sh: na 315.)

_*Zamuci gaba insha Allah!!*_
Rubutawa>>✍🏼
*Abubakar Salihu Kabara*

Gabatarwa_
_*ALHUSEIN ABBAN SUMAYYA*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
Post a Comment (0)