_*⚖️MATSAYIN ZAKKA A' SHARI'ANCE⚖️*_(4)
LOKACIN DA AKA WAJABTA TA:
DAKUMA KUMA WADANDA TA WAJABA AKANSU!!
Malamai sun yi sabani game da lokacin da aka wajabta Zakka.
Wadansu sun ce an wajabta ta ne a Makka.
Saboda ayoyin Makka wadanda suka yi magana a kanta.
Wasu kuma suka ce an wajabta ta ne a Madina.
Saboda ayoyin Madina sun fi bayyana wajabcin ta.
masu Magana ta biyu sun fi kawo hujja mai Karfi.
Inda suka ce musulmi a Makka daidaiku ne.
Basu da tsari zartacce.
Ba su da hukuma.
Ita kanta Zakkar ma ba ta da tsari wannan lokacin.
Watau ba ta da nisabi.
Ba a kuma ayyana wadanda za a bai wa ba.
Don haka maganar da ta fi rinjaye ita ce, an wajabta Zakka ne a Madina,
a shekara ta biyu bayan Hijira.
(Duba fiKhuz Zakkat na
Dr. Yusuful Kardawi,
Juz’I na 1 sh:52-62.)
WADANDA TA WAJABA A KAN SU:
Malamai sun hadu a kan cewa Zakka tana wajaba a kan Musulmi, baligi, mai hankali. Kuma wanda ya mallaki nisabi, tare da cika sauran sharuda.
Amma sun yi sabani a kan yaro da mahaukaci. Wasu sun ce ba ta wajaba a kansu ba.
Wasu kuma suka ce tana wajaba.
Amma magana ta biyu ita tafi Karfi,
saboda hadisai ingantattu da aiwatarwar sahabbai a kan haka.
Dabarani ya rawaito hadisi, kamar haka;-
"عن أنس بن مالك قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم، اتجروا في أموال اليتامى، لا تأكلها الزكاة.
Wato daga Anas (RA) ya ce, Manzon Allah (SAW)
ya ce: “Ku yi ciniki da dukiyar marayu, domin kada Zakka ta cinye ta”.
(Duba FiKhuz Zakkat juz’i na 1, sh:95 – 112.)
Wannan ya nuna cewa za a fitar da Zakka daga dukiyar yaro da ta mahaukaci.
_*Zamuci gaba insha Allah!!*_
Rubutawa>>✍🏼
*Abubakar Sadiq Salihu Kabara*
Gabatarwa_
_*ALHUSEIN ABBAN SUMAYYA*_
*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi
Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248