SUHUR ALBARKA NE


🌸 SUHUR ALBARKA NE 🌸

Sahabi Salman Alfarisi Allah ya Kara yarda dashi ya ruwaito hadisi daga manzon Allah sallallahu Alaihi wa sallama yana cewa "Albarka tana cikin Abubuwa guda uku; 
1. Jama'a
2. Thareed
3. Sahur". 
 Ø§Ù„كبير للطبراني ٦١٢٧.
 
Sahabi Abu Huraira Allah ya Kara yarda dashi shima ya ruwaito hadisi manzon Allah yace "Lalle Allah ya sanya albarka acikin sahur da kuma ma'auni". 
الجامع الصغير ١٧١٥
  
Hakanan Abdullah bin Haris ya ruwaito hadisi daga wani daga cikin sahabban manzon Allah yace; na shiga wurin manzon Allah yana suhur, sai yace "lalle suhur albarkane da Allah ya baku kada ku kyaleta". 
النسائي ٤/١٤٥

Sahabi Abu Sa'eed Alkhudry Allah ya kara masa yarda yace; Manzon Allah sallallahu Alaihi wa sallama yace "Cin suhur albarkane, kada ku bar yinsa koda kuwa da kurba dayane na ruwa, domin Allah mai girma da daukaka shi da mala'ikunsa suna salati ga masu yin suhur".
الجامع الصغير ٤٧٨٥

Sahabi Anas bin malik ya ruwaito hadisi, manzon Allah yana cewa "kuyi suhur domin acikin suhur akwai albarka". 
البخاري Ù¤/١٢٠ 

 Sahabi Jabir bin Abdillah ya ruwaito hadisi manzon Allah yace "Duk Wanda zaiyi azumi to yayi suhur koda da wani abune". 
مسند الإمام أحمد ٣/٣٦٧

Shaikh Ibnu Uthaimeen Allah ya masa rahama yana cewa akarkashin wadannan hadisan "Yana daga cikin albarkar suhur riko da umarnin manzon Allah, wanda riko da umarninsa alkhairi ne gabadaya.
     Sannan yana daga cikin albarkar suhur yana taimakawa akan ibadah, yana taimakawa mutum akan yin azumi".
 Ø´Ø±Ø­ رياض الصالحين Ù¥/٢٨٤.

#Zaurenfisabilillah 
Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah
Post a Comment (0)