_*⚖️MATSAYIN ZAKKA A' SHARI'ANCE⚖️*_(6)
HUKUNCIN WANDA YA KI BAYAR DA ZAKKA:
TARE DA FA'IDOJIN FITAR DA ITA:
Mai Kin fitar da Zakka iri biyu ne: Ko dai ya Ki bayarwa ne saboda bai yarda wajibi ba ce, Ko kuma ya Ki bayarwa ne saboda tsananin rowa da son abin duniya. Idan ya Ki bayarwa ne saboda bai yarda da wajibcinta ba, to ya kafirta. Idan kuwa don rowa ne, ko sakaci to fasiKi ne. Kuma hukuma za ta iya karba ta Karfi daga gares shi. Kamar yadda Khalifar Annabi (SAW), watau Abubakar (RA) ya yaKi wadanda suka Ki bayarwa a zamaninsa. (Duba Zakatul Ma’adni na Almukhtar bin Umar bin Al-Hussain As-Shankidi Sh:18-19).
Kuma ya kamata mu sani cewa, Kin bayar da Zakka yana sabbaba azaba mai muni ga mutum a lahira. Ga dai hadisin da Muslim ya rawaito game da haka:
عن أبي هريرة قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: "ما من صاحب كنـز لا يؤدي زكاته إلا أحمى عليه في نار جنهم فيجعل صفائح فتكوى بها جنباه ووجهه حتى يحكم الله بين عباده في يوم كان مقدار خمسين ألف سنة. ثم يرى سبيله إما إلى الجنة وإما إلى النار. وما من صاحب إبل لا يؤدي زكاته إلا بطح لها بقاع قرقر. كأوفر ما كانت تستن عليه كلما مضى عليه أخراها ردت عليه أولاها، حتى يحكم الله بين عباده في يوم كان مقداره خمسين ألف سنة. ثم يرى سبيله إما إلى الجنة وإما إلى النار. وما من صاحب غنم لا يؤدي زكاتها إلا بطح لها بقاع قرقر كأوفر كانت فتطؤه بأظلافها وتنطحه بقرونها ليس فيها عقصاء ولا جلجاء. كلما مضى عليه آخرها ردت عليه أولاها حتى يحكم الله بين عباده في يوم كان مقداره خمسين ألف سنة مما تعدون. ثم يرى سبيله إما إلى الجنة وإما إلى النار...".
Daga Abu Huraira (RA) ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce, "Babu wani mai taskace kudi, wanda ba ya bayar da Zakkarsa, face sai an Kona shi (kudin) a wutar Jahannama ya yi fadi sannan a dinga goga masa a gyaffansa da fuskarsa; har lokacin da Allah zai yi hukunci a tsakanin bayinsa, a yinin da yake kwatankwacin tsawon shekara dubu hamsin. Sannan a nuna masa hanyarsa, ko dai zuwa aljanna ko kuma zuwa wuta. Babu wani mai raKuma wanda ba ya bayar da Zakakrsu, face sai an jefa shi a cikinsu, a wani kwari mai fadi, cikakkunsu. Sannan su dinga bi ta kansa. Idan suka kai Karshe, sai a dawo da na farkon. Haka za a dinga yi masa, har Allah Ya yi hukunci a tsakanin bayinSa. A yinin da ya ke kwatankwacinsa tsawon shekara dubu hamsin. Sannan sai a nuna masa hanyarsa. Ko dai zuwa Aljanna ko zuwa wuta. Babu wani mai tumaki ko awaki wanda ba ya bayar da Zakkarsu, face sai an jefa shi a cikinsu, a wani kwari mai fadi, cikakkunsu, sannan su dinga taka shi da kofatansu, suna sukansa da Kahunnansu. Babu mai tanKwararren Kaho a cikinsu, balle marar Kahon. Idan suka kai Karshe, sai a dawo da na farkon. Haka za a dinga yi musu, har Allah Ya yi hukunci a tsakanin bayinsa, a yinin da yake kwatankwacin tsawonsa shekara dubu hamsin. Sannan sai a nuna masa hanyarsa, ko dai zuwa Aljanna ko zuwa Wuta…”. (Duba Nailul Audar na Shaukani, juz’i 2, sh:172-173).
FA’IDOJIN FITAR DA ZAKKA:
Mutane sukan dauka cewa fa’idar da ke cikin fitar da Zakka ta takaita ne kawai ga taimakawa talaka da dan abin da zai biya bukatunsa na wani lokaci. To ya kamata mu sani cewa lamarin fa bai tsaya a nan ba. Fa’idojinta suna da yawa kamar haka:
_*Zamuci gaba insha Allah!!*_
Rubutawa>>✍🏼
*Abubakar Salihu Kabara*
Gabatarwa_
_*ALHUSEIN ABBAN SUMAYYA*_
*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi
Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248