TSOKACI AKAN ZAKKAR FIDDA KAI

*TSOKACI AKAN ZAKKAR FIDDA KAI*
Abdullahi Dan Abbas (RA) yace: “Manzon Allah (SAW) ya farlanta zakkar fidda kai, Saboda tsarkakewa ne ga mai azumi, daga maganganun da ba su dace ba, kuma abinci ne ga miskinai” 

Abdullahi Dan Umar (RA) kuma cewa ya yi: “Manzon Allah ya yi umurni da zakkan fidda kai ga yaro da babba da Duk wadanda kuke kula da su” (Riwayar Daru Kudniy).

Don haka mai gida Wanda yake da hali zai ba da nasa da na Matansa, yaransa, da duk waɗanda suke ƙarƙashinsa, Sun yi azumi ne ko ba su yi ba, don faranta ran talakawa da miskinai ranar sallah kada su je bara ko roƙo, ana cikin farin ciki su kuma suna baƙin ciki, shi ya sa aka ce a ba su don a faranta mu su rai.

         *ABIN DA ZA A BAYAR:* 
Za a bayar da Sa’i guda ne na kowane mutum Daya, daga dukkan nau’in abin da ake kiransa abinci, ba lallai sai dabino ko Alkama ba, wannan shi ne bayanin da malamai suka tabbatar.

Don haka za a iya bayar da sa’in dawa, gero, masara, shinkafa da garin hatsi, ko na kwaki, matuÆ™ar dai abinci ne babu laifi.

         *LOKACIN FITARWA:* 
Ana bayar da wannan Zakkar ne ana gobe sallah kafin a fita zuwa Masallaci, kamar yadda Hadisin É—an Umar (RA) ya nuna cewa “Manzon Allah ya yi umarni da bayar da zakkan fidda-kai kafin fitan mutane zuwa masallaci” (Bukhari da Muslim).

          *WANDA ZA A BA WA* 
Za a bawa miskini ne ko faƙiri wanda ba ya da hali, kamar dai yadda Annabi (SAW) ya ambaci lafazin Miskini, to shi ne za a ba shi, ba lallai sai an rarraba ga wadanda aka ambace su a cikin Ayar Zakka ba.

Adda'u Waddawa Social Media 
27/Ramadan/1441
20/May/2020

Post a Comment (0)