NASIHOHI 30 GA 'YAR UWA MACE


NASIHOHI 30 GA 'YAR UWATA MACE

1. Ki dena kula kowanne irin saurayi, ke ko da wani ya zo ya ce yana son ki ki duba rikon sa da addini, kada ki ce sai mai kudi. Wai har wani lissafi mata suke yi ga mazajen da suke zuwa wajen su, idan suka ce "A" accounter "C" chairman "T" Teacher, ba sa son mai "T" ya zo wajen su, domin kuwa malamin makaranta ne, amma wannan tunanin wasu matan ne, wasu kuwa babu ruwansu da duk wanda ya zo gare su matuqar mai tarbiyya ne.
.
2. Kada ki riqa rokon saurayinki kudi ko wani abu na daban, ke ko da kuwa za ki nemi wani abin a wajensa kada ki yawaita. Rokon da kike yi wa saurayinki zai kai ga bude kafar barna har ya fara tunanin bin wata hanyar don fanshe abin da ya ba ki.
.
3. Idan Allah ya kawo miki saurayi matuqar dai yana da kyawawan halaye ki riqe abinki gam, kada ki tsaya wasa, dora buri a kan saurayi ba abin yi ba ne gare ki.
.
4. Ban da wulaqanta mutumin da ya ce yana son ki, idan kina da wanda kike so ki fada masa zance mai dadi wanda ba zai tafi da haushinki ba.
.
5. Ki yi hakuri da abin da ke faruwa da ke, wata macen tana kuka da idan saurayi ya nuna yana son ta har takai ga tafiyarsu ta yi nisa sai ya zame ya bar ta. Ki ci gaba da rokon Allah ya ba ki miji na gari.
.
6. Ki dena yin dare kina yin hira da saurayi. Me zai hana ki yi hira da yamma ko wani lokaci na daban wanda ba dare ba, ko dai kina ganin hirar yamma, rana da safiya kauyanci ce?
Me ya kai wannan kauyanci; saurayi da budurwa su riqa yin hira har karfe goma zuwa sha daya na dare su kadai suna aikata abin da suka so sashen jikkunansu?
.
7. Samarin banza na 'yan matan banza ne, haka 'yan matan banza na samarin banza ne, babu yadda za a yi saurayin banza ya zo wajen ki ba tare da kin gane shi ta wata hanya ta daban ba saboda zai nuna asalin munanan halayensa da manufar da ta kawo shi wajen ki a fili ko bayan soyayyarku ta yi karfi.
.
8. Allah ne kadai ya san irin abin da samarin banza suke yi a wajen hirar dare da 'yan mata. Takai da saurayi babu inda baya tabawa a jikin budurwarsa. Wata take cewa saurayin kawarta ya kai da har yatsarsa yana sanyawa a gaban kawarta wai jima'i ne kawai ba sa yi, wata kuwa cewa ta yi idan saurayinta ya je wajen ta suna biyawa kansu buqata ta hanyoyi daban-daban.
.
Tir da samarin da suke lalata da yaran mutane. Wai kuma a haka samarin suke hurewa 'yan mata kunne su ba su hadin kai su yi abin da suke so za su aure nan gaba kadan, wannan karya ce, mafi yawan samarin ba sa auren ire-iren 'yan matan da suka lalata da kansu, karshe ma idan aka ce su aure su sai sun ce "ba za mu aure su ba, su din lalatattu ne" yo akwai wadanda suka lalata su in ba su ba?
.
Yanzu ba abin mamaki ba ne ka ji an ce wance 'yar gidan Alhaji ko Malam wane an yi mata cikin shege. Ga shi nan dai ana samun yawaitar 'yan mata da cikin shege su ki fadar na saurayinsu wane ne sai an takura su, wata kuwa ana tambayar ta take bayar da amsa kai tsaye babu ruwanta.
.
9. Kada ki yarda son abin duniya ya rufe miki ido ki auri mai kudi ki watsar da talaka mai addini. Lallai idan kika yi haka za ki yi kuka da idonki nan gaba.
10. Allah ne yake azurta wanda ya ga dama a lokacin da ya so. Wanda ya ce yana son ki amma ba shi da kudi ba shi ya hana kansa ba kuma bai isa ya azurta kan nasa ba.
.
11. Idan za ki fita daga gida zuwa wani waje na daban kada ki bayyana surarki, kada ki fesa turare mai kamshi in ban da wanda yake kashe warin jiki, kuma kada ki fitar da gashinki waje. 
12. Macen da ta sanya hijabi tafi samun tsaro fiye da wace take tare da 'yan sanda suna gadinta.
.
13. Sanya cikakken tufafin muslunci yana kara girma, mutumci da karamci a idon bayin Allah mai rahama. Idan mutum ya ga wani dan iska ya ci kwalar mace mai cikakken kayan muslunci zai ce sake ta ko na..... Amma da zai ga mace da kayan banza da namiji ya shake ta a kan hanya ba lallai ba ne ya ce "sake ta" idan ma zai ce zai iya tambayar sa dalilin shakewar. To dama 'yar iska plus dan iska is equal to 'yan iskas.
.
14. Ki suturta muryarki, kada ki riqa daga murya yayin da kike yin hira da kawayenke, mijinki ko 'yan uwanki.
15. Ki san irin hirar da ta dace da wace bata dace ba.
.
16. Ban da zagi da cin mutumcin mutane, ki girmama na gaba da ke, ki kyautatawa 'yan tsararki kuma ki tausayawa na kasa da ke.
17. Ki bi umurnin iyayenki matuqar ba na sabon Allah ba ne, ki hanu daga abin da suka hana ki. Mai sabawa iyaye da zaginsu ba zai shiga Aljannah ba.
.
18. Da zarar kin gane kawarki wance ta banza ce, ta fiye kula samarin banza ki yi mata nasiha idan ta ki ji ki dakile kawancenki da ita.
19. Abota tsakanin mace da namiji tana kaiwa ga sabon Allah, to ki kula sosai kada ki yarda wani ya fake da cewa ke kawarsa ce ya zo yana yin lalata da ke.
.
20. Ki kyautatawa mijinki, kada ki ki bin umurninsa da kin hanuwa daga abin da ya hana ki matuqar ba na sabon Allah ba ne. Biyayyarki da kyautata masa za ta kai ki ga samun aljannah madaukakiya.
.
21. Kada ki biyewa social media domin kuwa za ta iya yin sanadiyyar rabuwarki da saurayinki ko mijinki. Da yawa daga cikin 'yan mata sun rabu da samarinsu ta dalilin social media, haka ma matan aure sun rabu da mazajensu wasu kuwa ba su rabu ba sai dai mummanan zato ya shiga tsakani hakan ya sa auren ya ki yi wa kowanne daga cikin su dadi.
.
22. Ki dage da sallar farilla, ki kiyaye farjinki daga zina sai ki sami babban rabo a nan Duniya da kuma Lahira.
23. Ban da yin mummunan zance da jifar mutane da abin da ba su ji ba ba su gani ba.
.
25. Idan aka kawo miki labarin wani laifi ko wani abu da saurayinki ko mijinki yake yi ki yi bincike don ki tabbatar da gaskiyar labarin da aka kawo miki. 
26. Ki koyi karatun Alkur'ani, idan kika koya ki koyar da wadanda ba su iya ba sai ki zama wace tafi kowa alheri a cikin al'ummar Manzon Allah saw.
.
27. Ki mayar da hankali wajen koyon tsarki, sallah da azumi tun kafin ki yi aure sai komai ya zo miki da sauki bayan kin yi auren.
28. Ki riqa yin azkar na safe da yamma a kowace rana, kuma ki riqa yi wa Annabi salati mafi karanci guda ashirin a kowace rana; goma da safe goma da yamma.
.
29. Ki yawaita yin Istighfari, kada ki ce ba ki aikata wani laifi ba don haka ba wani Istighfari da za ki yi, hakan ba hujja ba ce. Allah yana son masu tuba saboda haka ki yi kokarin zama daya daga cikin wadanda Allan yake so ta hanyar yawaita Istighfarin.
.
30. Ki bayar da gudunmawarki ga 'yan uwanki mata don kawo ci gabansu ta hanyar koyar da su karatun Alkur'ani, Hadith, Fiqhu da Tauhidi in kuwa kin iya sana'o'i 'yan uwanki mata na buqata, ki koyar da su kyauta ko ki sanya musu wani abu da za su riqa biyan ki.
Post a Comment (0)