ILLOLIN DA SHAN RUWAN SANYI KE YI WA MATA


*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Illolin Da Shan Ruwan Sanyi Ke Haifarwa Ga Ya Mace_*

Yar uwa ki guji amfani da ruwan sanyi a wajen tsarki da kuma yawan shan ruwan sanyi, domin yana ma mata illa a ciki, hatta ko da karamar yarinya ne a guji yawan yin mata amfanin da shi, don ba yanzu ake ji ba, gaba.

Da wannan ne na ke jan hankalin ‘yan uwana mata da mu guji yawan amfani da ruwan sanyi, domin ruwan sanyi yana da illa. 

*Ga Kadan Daga Cikin illolin Shan Ruwan Sanyi:*

*1. Tsaida Bugun Zuciya:* Bugun zuciya shi ke gyara dumin jiki da dai-daita numfashi, to ruwan sanyi yana sa bugun zuciya ya rika raguwa har takai ga tsayawa. 

*2. Lalata Tsarin Kayan Ciki:* Shan ruwan mai sanyi yana tattare hanta guri daya sai ya sanya abinci ya ki narkewa da wuri, hakan ke jawo matsalar hanji (Ulcer) ke nan ko kuma tashin zuciya. Yawan zub da yawu ko tashin zuciya ko kuma saurin kullewar ciki.

*3. Dauke Karfin Jiki:* Duk da cewa shan ruwan sanyi kan sa mutum ya ji dadi, amma a hankali yana dauke masa karfin jiki sakamakon lokacin da ruwa mai sanyi ya shiga jikinsa dole sai na’urorin jikin sun yi kokarin ganin sun maida wannan ruwan ya dai-daita da dumin jikin, hakan yana sa su yi rauni sakamakon kokarin da suke yi yana wuce haddi. Ko kun lura duk sanda kuka sha ruwan sanyi sai kun ji duk jikinku sanyin ya ratsa kaman farkon zazzabi a hankali kuma sai ku ji ya daina.

*4. Ciwon Makogwaro Da Dakushewar Murya:* Yawan amfani da ruwan sanyi yana lalata jijiyoyin makogwaro har su kai ga ba sa amfaninsu yadda ya kamata. Idan mutum ya kai shekaru 40 yana san ruwan sanyi sai ya fara fama da ciwon makogwaro da dakushewar murya ta fashe kwatankwacin mashayin taba.

*5. Ciwon Hanta Da Koda:* Dukkan su suna bukatar wadataccen ruwa a jikinsu, don haka yayin da mutum ya zama yana amfani da ruwa mai sanyi zai zamo su kuma suna cutuwa ta yanda aikinsu zai fara kasa, indan haka ta samu mutum ya shiga mastala.

*6. Busar Da Ruwan Jiki:* Akwai na’urori a jikin Dan’adam da aikinsu shi ne, sadar da ruwa ko’ina na jikinsa zai samu damar motsawa cikin nishadi. To wadannan na’urori su kan yi sanyi sakamakon ruwan sanyi sai su zama jikin ba kwari.

*7. Matsalar Ma’aurata:* Wannan abu ne tabbatacce har ga likitocin zamani cewa, shan ruwan sanyi yana raunata mazantakar namiji yana kuma busar wa mace in mahaifarta na da rauni yana iya hana haihuwa. Yana tsinka maniyyin namiji ya zama yana saurin biyan bukata ko kuma na rage masu kuzari. Yana dauke ni’imar jiki su zamo ba sa gamsuwa da juna.

*8. Basir Da Ciwon Kai Na Gefe (Migraine):* Shan ruwan sanyi kamar yanda na ce muku, yana tattare hanji hakan yana kawo mutum ya kasa bayan gida sai ya hadu da basir. Sannan yana kawo ciwon barin kai wanda ake cewa ‘migraine’. Shi kuma ‘migraine’ yana kashe jijiyoyin jikin ido a ta yadda za a daina gani sosai, indan ma yayi nisa har hauka yana sawa.

Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*
Post a Comment (0)