RAMADAN A GIDAJENMU 1


🌻 *RAMADAN A GIDAJENMU {01}*🌻

بسم الله والصلاة والسلام على رسول الله وآله وأصحابه أجمعين. 

Tace dalilin da yasa nafi kaunar mijina a watan Ramadan shine: Saboda yana yin iya kokarinsa wajan yaga cewa bai kawo mana *haram* gida domin muyi sahur ko bude-baki da shi ba, 

Yana tausayamin kuma yasanyamin Albarka idan yaga ina aikace-aikacen gida, kuma yana yabamin idan nayi wata bajinta..

Abinda ma yafi burgeni da shi shine yana kau da kansa akan wasu kusakurai na kuma yabani uzuri saboda yasan muna cikin watan Ramadan,

 Kuma yana ragemin wasu aikin idan yaga sunyimin yawa sai yatayani muyi tare, saboda Shima yanaso yatarar kyawawan ayyuka a wannan watan.

_"Qalubalenmu, lallaikam wannan hali anasonshi ga kowane namiji aciki da wajen wannan watan mai Albarka."_

_"Allah yakarbi ibadunmu kuma yasanya mu cikin yantattun bayinsa a cikin Wannan watan mai Albarka."_

✍🏻 *Idris M Rismawy*
Rismawy86@gmail.com
Post a Comment (0)