FARINCIKI


*FARIN CIKI*

Wata irin ni'ima ce da mutum ke yima kansa sanadin samunta ko rasa ta, tana daga cikin abubuwan da suke dawowa mutumin da yasanya wani cikinsu. 

Matukar ka sanya wani cikin farin ciki, to kaima sai Allah ya sanya ka farin ciki, matukar kana yiwa wani fatan Farin samun farin ciki, kai ma zaka dace da farin cikin. 

Rayuwarka takan iya samun farin ciki, a lokacin da zuciyarka taji ba ta jin haushin wani yayin da yashiga cikin farin cikin, ba ta yi masa kushe, hassada ko jin haushin rabon da Allah yayiwa waninka, yabashi abinda bai baka ba. 

Idan kakara waigawa zakaga kaima ya baka abinda bai bashi ba, kayi na'am da hukuncin Allah, kar ko kusa kanuna Allah bai iya hukunci ba, domin jin haushin haka kana nuna yin zanga-zanga ne da rabon da Allah yayi. 

To wai ma, wa nene zaifi Allah iya rabo na Adalci,? Wa ya isa yaraba abinda Allah bai raba shi ba? Lallaikam mutum zai iya yin bankwana da Imaninsa matukar zuciyarsa na raya masa akasin abinda yadace Mummuni yayi. 

Allah yarabamu da cutar Hassada da kuma sharrin masuyinta, yakara tsare mana imaninmu kuma yasa mucika da kyau da imani. 

✍🏻 *BIN YA'AQUUB*
Post a Comment (0)