TSAKANIN MU DUK DA BANBANCINMU 11


*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//11📿*

*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*

Malam Shaukaniy RL yake cewa "Sau tari za ka taras masana guda biyu da suka sami sabani a kan wata mas'ala, kowa ya koma bincike kuma ya tsaya kan fahimtarsa, sai ka ga 'yan ba ni na iya har sun san cewa wane ne da gaskiya wancan kuma 'yan hujjojin da ya kawo ba su wuce cikin cokali ba, shi irin wannan bangarancin yakan faru ne har cikin daliban ilimi ma, masamman in ya kasance a cikin jama'a, da wahala ka ga maras gaskiya ya karbe ta hakan kan faru ne a wurin karatu da matattarar ilimi (Adabut Tibb p81)".

*GINSHIQI NA GOMA*

BANDA WUCE QIMA

Dole dai ya kasance ba a wuce gona da iri ba wurin raddi, yadda za a shiga cikin haqqin juna, kowa zai iya fadawa cikin kuskure, da gangan dai masanin Allah, masanin azabarsa ba zai jefa mutane cikin halaka don shi ma ya bi su su halaka tare ba, amma kasancewar mutum dan adam ne, gajiyayye zai iya sakin hanya bai san ma ya yi ba, a zatonsa shi ne ke kan daidai, in mu ma mun hango kuskuren to fa abinda yake nemannan shi muke nema, babban abinda ya dace sai mu janyo shi kan hanya don ya koma shiryar da mutane ba batar da su ba.

Wannan gagarumin aiki da za mu yi muna da lada, ladar shiryarwa ga ta sanya mutum cikin aikin da Allah ke so, duk lokacin da ya aikata abin alkhairi muna lada, sai dai abin takaici in wani da muke ganin ya saki hanya ya abka cikin kuskure kuma yana qoqarin fitowa ba ma janyo shi a jiki, ba ma taimakonsa, sai ka ga mun dage wajen nisanta shi da bakunanmu da alqalumammu, in ya dan kwano ya fadi daidai mu ce "Borin kunya ne ko wuta ya ji dan nema" ga amfani da kakkausan harshe, ba wani qoqari ba muke yi na janyo shi a jiki bare mu kame hannunsa daga barnar da yake ciki, raddi kam dole ne, amma akwai hanyoyi da dama da za a bi wadanda burimmu dai shiriyarsa ne ba muzanta shi da qoqarin ganin qarshensa ba, wasu har zagi da cin mutunci za ka ji suna yi, wadanda mutanen qwarai ne bai dace a ji irin wadannan lafuzzan a bakunansu ba.

In muka ga kuskure ya zama dole mu gyara ba tare da kambama shi ba, bare kuma mu kai mutum inda ma bai kai ba, mu ba shi wata sifa ta daban, misali "Tunda ya ce kaza to kaza yake nufi kenan, in kuwa ya zama kaza to ba tantama kafiri ne ko fasiqi ko mushriki ko dan bidi'a" wadanda za su dauki maganar kamar almajirai ko masu saurare sai su qara wa maganar gishiri su yanke abinda suke ganin shi ne daidai a wurinsu, irin wannan sam bai dace ba koda akwai sabani a aqida bare wanda kuke gani aqidarku daya ce ya dai fandare ne, idan likita zai koma cewa "Duk wanda ya dauko cuta da gangan ya yi me ya sa ya jajubo ta ku yi maganinsa (ba maganin cutar ba) gobe ya qara" wannan ba likitan gaskiya ba ne.

In ka ji yana tambayoyi da bincikar baya, yana lalubo hanyar gyara ne nan gaba da samun maganin cutar, Ibn Taimiya yake cewa "In ka duba galibin sabanin da ake samu a tsakanin al'umma a yau, malamansu, masu bauta cikinsu, shugabanninsu, da sarakuna za ka taras mafi yawanci ta'adi ne wajen yin tawili ko ba tare da tawilin ma ba, kamar yadda Jahamawa suka fitini ahlus Sunna kan sifofi da abinda ya shafi Qur'ani, ko ta'adin Khawarijawa kan Aliy RA da Iyalan gidansa [Wanda Shi'a ke fitinarmu da qiyayyar Aliy RA da Iyalan gidansa, duk sanin bambancimmu da Khawarijawan], ko ta'adin masu sifanta Allah da wasu halittu kan masu tsarkake shi, ko kamar yadda wasu ahlus sunnan ke yi, kodai su abka wa junansu, ko su sifantu da 'yan bidi'a wajen qarin gishiri (Al-Fatawa 14/482-483).

Al-Qarafi yake cewa dangane da sharuddan yi wa mutum raddi "Ya yi qoqarin kore nau'ukan barna daidai iyawarsa da sharadin kar ya qetare gaskiya, kar ya jingina wa mutane abinda ba su taba yi ba na fasiqanci da barna, ya tsaya a kan abinda yake gargadi a kai kawai, kar a ce wa wani dan bidi'a: Yana shan giya, ko yana zina ko makamancin hakan wanda a zahiri ba ya yi (Al-Furq na Al--Qarafiy 4/207-208)" abin takaici ba 'yan Shi'a da aka kwashe musu albarka ba hatta wasu dake da'awar ba sa shi'an, suna bin wasu salihan bayi ne, haka za su saka Yazeed bn Mu'awiyya a gaba, su yi ta zagi, sukarsa da shaye-shaye ko neman mata ba tsoron gamuwa da mahalicci, wai kuma a dole koyarwa ake yi ko raddi ga mabiya Sunnar ma'aiki, Allah ya sa mu dace.

*GINSHIQI NA SHA DAYA*

ME YA BAYYANA?

Abinda ya dace kenan mutane su tsaya kan abinda ya bayyana a zahiri, misali za ka yi tauna-tauna da wanda ake ganin ya saki hanya, to ka tsaya kan abinda ya bayyana na abinda ake sukarsa da ita, ba wai wanda ake zaton cewa niyyarsa kenan ba tunda galibin masu aqida irin tasa abinda suke yi kenan, masamman in bai karbi aqidar da ake qoqqarin daura shi a kai ba, idan ya fito da wata magana wace tabbas ta dace sai mu karba, koda kuwa muna ganin ya boye wani abu bai fada ba, sai dai in mun sani a aqidarsa akwai yuwuwar wannan qaryar, to sai mu karba da taka tsantsan, kamar dai 'yan Shi'a, mun san suna da abinda suke kira Taqiyya, mu a aqidarmu wannan qarya ce tsagwaro, babbar zunubi ce a cikin manya, ba a karbar maganar mai yin ta, su kuwa addini ce ma har lada ake samu in an yi.

A muslunce akan yi ma'amalla da mutum ne kan abinda ya bayyana, wanda ya boyu kuma sai mu maida shi ga Allah SW, shi zai yi sakamako a kansa ranar qiyama, mu kam iyakarmu mu yi mu yi qoqarin qwato mutum ba mu tura shi ba, ga shi ma Annabi SAW ya karbi tubar munafuqai da suka yi ta shiga muslunci tare da saninsa cewa galibinsu munafuqai ne koda ba dukansu ba, irin wadannan dabi'u na Annabi SAW su za mu koya a duk lokacin da muka sami kammu a wurare masu kama da wannan.

Zamuci gaba insha Allah.

*Gabatarwa: Zauren Sunnah*
Post a Comment (0)