RANA IRIN TA YAU A TARIHIN MUSULUNCI DA BA ZA A TAƁA MANTAWA BA


*🗓 RANA IRINTA YAU A TARIHIN MUSULUNCI DA BA ZA'A TABA MANTAWA BA*

A rana irinta yau 17 ga Ramadan, shekara ta biyu bayan Hijira (17/Ramadan/02) wanda yayi daidai da 13/March/624 akayi wannan shahararren yaki a tarihin Musulunci wato yakin ⚔ *Badar*, tsakanin rundunar Manzon Allah (s.a.w) da matasan Sahabbansa, da kuma Rundunar Mushrikan Quraishawa karkashin *Amru bn Hisham wato (Abu Jahal)*. 

Rundunar Manzon Allah (s.a.w) dauke take da matasa masu kananun shekaru, wadanda yawancinsu yan shekaru ashirin da kadan ne, sai yan talatin da kadan, kusan dukansu yara ne. 

Yau da yin wannan yakin shekaru dubu daya da dari uku da tis'in da shida (1,396) a kalandar rana, wanda yayi daidai da shekaru dubu daya da dari hudu da talatin da tara (1,439) a kalandar wata.

Asalin wannan yaki ba shirin yaki wadannan matasan Musulman suka yi ba. Sun ji *Abu Sufyan* ne (lokacin bai Musulunta ba) yana dawowa daga *Sham (Syria)* ya nufi *Makkah*, da dukiyar da aka kwace daga hannun Musulmai aka koresu daga Makkah, don haka suka fita domin karbar dukiyarsu, amma Abu Sufyan ya ji labari, don haka ya gudu musu, ya kuma aika sako zuwaga Mushrikan Makkah ya sanar da su abinda ake ciki, su kuma suka fito da nufin yaki, tare da su akwai Mayaka dubu da wani abu, domin yakar matasan Musulman da ba su fito da niyar yaki ba, wadanda gaba dayansu su dari uku ne da kadan.

An kashe mutane saba'in daga cikin Mushrikai, har da shugabansu Abu Jahal, aka kama wasu saba'in din. Su kuwa Musulmai an kashe mutane goma sha hudu ne kadai, 8 daga Ansarawa mutanen Madina, 6 daga Muhajirai mutanen Makkah.

Badar dai sunan guri ne, da ke tsakanin Makkah da Madina. Tsakaninsa da Makkah a mota 🚘 a yanzu kilometer 343 ne (kusan nisan da ke tsakanin Gombe da Kano) amma tsakaninsa da Madina kilometer 143 ne (kusan nisan da ke tsakanin Gombe da Bauchi).

Wannan hoto 🖼 da ke kasa, yana nuna inda Badar yake a halin yanzu.

Wadannan matasan su suka bada jininsu da dukiyarsu suka tsare addinin Musulunci suka yadashi har ya iso garemu. Lallai Allah Ya yarda da su, su ma sun yarda da Shi.

*❓SHIN ME KAI KUMA KA YIWA MUSULUNCI DA ZAI YI ALFAHARI DA KAI, GASHI KO KARAMIN YARO KA TAMBAYA YA TABA JIN KALMAR BADAR*❓

Abu Albani
17/Ramadan/1441
10/May/2020
Post a Comment (0)