RUFE MASALLATAI DOMIN GUDUN YAƊUWAR CORONAVIRUS


RUFE MASALLATAI DOMIN GUDUN YAƊUWAR CORONA VIRUS, HAKAN YA SAƁAWA SUNNAR ALLAH DA MANZON ALLAH (S.A.W) 

           0️⃣0️⃣1️⃣

Annabi Muhammad Mai Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata Agare Shi. Yana Cewa Babu Wani Cuta Mai Kama Mutum da Kanta Sai da Izinin Allahu Swt. Duba Cikin ( Silsilatus Saheeha 1152). Idan ANNOBA ta Auku a Kasa Ko Jiha, toh Kai Tsaye Ana Komawa Ne Zuwa ga Allah da Yin Ibada Sosai da Neman Gafaran Allah Domin ya Sassauta mana ya Kawo mana Saukin Wannan Masifar da aka Faɗa Cikin sa.
        Domin Babu Abinda Yake Ɗauko ANNOBA ya Sauka a Cikin Al'umma illa Aikata Fasadi da Yawan Aikata Zunubai, Zina-zinace Yin Luwaɗi Mata da Maza Dukka, Aikata Alfasa Shaye-sheye Zalunci Almubazaranci da Dukiya, Shuwagabani Marasa Adalci, Cin Hakkin Marayu etc. Aikata Waɗannan Abubuwan a Bayan Kasa a Mai da komai ba komai ba, Shiyasa Sai Allah Ya Aiko da Hukuncin Shi na Annoba Din. 
    Sannan Idan Za'a Koma Zuwa ga Allah a ina ne Ya Dace a Je? Shine Ɗakin Allah Masallaci. Toh Sai aka Ce a Kulle Su Domin kada Jama'a Su Yaɗa ANNOBA. Innalillahi. 
       Ita ANNOBA Bata Taɓa Chanja Wani Dokar Allah da Ya Aiko, Sannan Shi ANNOBA Bai Taɓa Chanja Wani Sunnar Annabi Muhammad Mai Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata Agare Shi. saboda Haka Wai Ace a Kulle Masallatai. 
      Kenan Wannan ANNOBAR ta Chanja Hukuncin Allahu Swt, Ace Wai Idan Za ayi Sallah a Masallaci toh Ayi Sahu Nayin Sallah Din a Samu Distance na Meter 1. Don Allah Wanne Irin Sahu ne Wannan? Kamar Na Coci. Kenan Wannan ANNOBAR ta Chanja Sunnar Manzon Allah da Yace a Haɗe Sahu Kib. Ace Wai Musulmi Ba Zai Yin Musabaha da Ɗan Uwan Shi Musulmi ba, Anan Ma ANNOBA ta Chanja Sunnar Manzon Allah.

Wallahi Duk Wani Malamin da Ya Bada Fatawar Cewa a Kulle Masallatai Domin Cutar Annoba Kada Ya Yaɗu a Cikin Al'umma. Toh Wajibi Ne Gare Shi Ya Shiryawa Kansa Amsa Tun Kafin Ya Mutu. Domin Wajibi ne Gare Shi Sai Yayiwa Allah Bayani. Duba Cikin ( Bakara Ayata 113) Allah Yana Cewa Waye Yafi Zalunci Akan Mutumin da Ya Hana Masallatan Allah, Yace a Kulle Masallatai a Daina Yin Zikirin Allah a Cikin Sa, a Daina Yin Sallah, a Daina Yin Ɓautan Ubangijin Allah a Ciki.
       Anan Kokarin a Ruguza Masallaci da Musulmai Baki Ɗaya. Kafirai Makiya Allah Makiya Manzon Allah, Sun Gwada Ku Sun Gane Cewa ba Ku San Darajan Addinin Ku ba. 

Yaya Za'a Ce Wai a Daina Yin Ɓautar Ubangijin Allah Madaukakin Sarki a ta Dalilin Samuwar ANNOBA? Domin ga Abinda Allahu Swt Ya Ambata Mana a Cikin Suratul Bakara Kamar Yadda Mukayi Bayani a Sama. 
      Wallahi Duk Mutumin da Yayi Dalili Yace a Kulle Masallatai a Daina Yin ibada a Cikin Su Domin Kada a Yaɗa ANNOBA, toh Sai Allah Ya Kunyata Shi Kafin Ya Bar Duniya, wai Domin ANNOBA Kayi Sababin a Rufe Masallatai ana Hana Bayin Allah Yin ibada a Ciki, Toh Allah Yayi Alkawarin Sai Ya Kunyata ka Tun Anan Duniya, Allah Yace a Lahira Kuma Inada Azaba Mai Raɗaɗi, Allah ya Tsare Ameen___


Mu Hadu a Rubutu Na Gaba In Allah ya Kaimu Lafiya. 


Daga Zauren Muslim Women Mata Zallah Whatsapp Group. 


MUHAMMAD TUKUR JALINGO 
Domin Shiga Wannan Group Ki Turo Mana Da Cikakken Sallama Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Kai Tsaye Ta Whatsapp Number Namu Kamar Haka 
(08164223447) Ko (08151796429) 
This Group Is Only For Women Please.
Post a Comment (0)