*🍝 GIRKE-GIRKEN ZAMANI 🍝*
*SEASONINGS AND SPICES //3*
*10. Knorr cube:* A gaskiya a da babu abun dandanon da aka aminta dasu kamar Maggi da Rayco amma a ganina knorr ya taka su, don gaskiya idan mace ta san sirrin knorr ba zata sake saka wani maggi star in bashi ba, amma wani lokacin sabo da abubuwa shi yake hana mu gwada wasu. Duk da kowa akwai abun da yake so kuma yake amfani dashi.
*11. Onga cube:* Cube da onga idan aka hada shi da knorr shima yana bada ma’ana sosai yan'uwa.
*12. Masoro (black pepper):* Duk da masoro anfi sashi a cikin su koko su kunu a haka muka dauke shi, amma ana saka shi a girki, sai ki hada shi a cikin kayan kamshin ki. Kuma ana sanya shi a cikin kayan shayi. Amfanin sa a bangaren lafiya shine yana hana tari da mura, yana taimaka wurin digesting proteins na abinci, yana gyara haqori, yana preventing cancer heart disease dama sauran su.
*13. Cinnamon (girfa):* Shi ma ba za’a barshi a baya ba, ana saka shi a girki duk da dai ni bana sakawa, ana saka shi a cikin wasu drinks, sannan ana sashi a cikin snacks kuma ana sashi a kayan shayi. Shima yana kamuwa da diabetes, zuciya, haqori, da blood pressure dama sauran su.
*14. Nutmeg (gyadar miya):* To naga dai mutane suna amfani dashi, especially a snacks but ni dai bana amfani dashi, shi ma yana taka rawa wurin qayata abubuwa.
*15. Mr Chef Cube:* Ban taba amfani dashi ba amma shima mata dayawa naji suna yabon sa a girki.
Duka abubuwan da nake rubutawa na gargajiya ana samun na kanti wanda kin huta yin daka.
*✍Written by admins*
*Sumayya &*
*Fauziyya*
*🍝 Girke-Girken Zamani 🍝*
*WhatsApp Group*
*0816 772 2658*
*0803 466 1023*
