SHARHIN FIM ƊIN BIGIL


SHARHIN FIM ƊIN BIGIL 


Bigil fim ɗin India ne da ya fita a cikin shekara ta 2019. Shiri ne da aka shirya shi a cikin harshen Tamil kuma yana ƙunshe ne da faɗa tare kuma da wasan ƙwallon ƙafa. An sanar da tabbacin cewa za'a yi wannan shiri ne a ranar 14 ga watan Nuwambar shekara ta 2018 inda a wancan lokaci ake wa shirin take da Thalapathy 63. Haka kuma shirin shi ne shiri na uku da jarumi Vijay yayi da mai bada umurni Atlee bayan Theri da kuma Mersal. 

An fara ɗaukar wannan shiri ne a ranar 21 ga watan Janairu 2019 a garin Chennei, yayinda kuma aka kammala a ranar 10 ga watan Agustan wannan shekara. Haka kuma an sanar da sunan shirin ne a ranar 22 ga watan Yuni na 2019 tare da hoton farko na shirin. Ma'anar Bigil dai shi ne fito. 

An fassara wannan shiri tare da sakinsa a cikin harshen Kannada da sunansa na asali, yayin da aka fitar da shi a harshen Telugu da sunan Whistle. Fim ɗin ya samu yabo kuma ya samu suka a lokacin fitarsa. Sai dai kuma ya samu nasara sosai a harkar kasuwancinsa domin kuwa ya samu damar zama fim ɗin harshen Tamil da ya fi kowanne kawo kuɗi a 2019 domin kuwa ya kawo kuɗi kimanin crore ₹285-300 a yayin fitarsa. Hakan ya sa ya zama fim ɗin Indiya na biyu da ya fi kowanne kawo kuɗi a shekarar, sannan kuma ya zama fim ɗin Vijay da ya fi kowanne kawo kuɗi tun bayan shigowarsa harkar fim. Fim ɗin ya cika kwana ɗari da fara haska shi a gidan wasan kwaikwayo a ranar 1 ga watan Fabarairu 2020. Na ba shirin tauraro 4.5


• Bada Umurni: Atlee Kumar

• Ɗaukar Nauyi: Kalpathi S. Aghoram
Kalpathi S. Ganesh
Kalpathi S. Suresh

• Labari/ Rubutawa/Tsarawa: Atlee Kumar

Sautin Waƙoƙi: A. R. Rahman

• Sautin Shiri: A. R. Rahman & 
Qutub-E-Kripa

Horas da 'yan wasa: G. K. Vishnu

• Tacewa: Ruben

• Kamfanin da ya shirya: AGS Entertainment

• kamfanin da ya yaɗa: Screen Scene Media Entertainment

• Ranar Fita: 25 October 2019 

• Tsayin Shiri: Mintuna 178 

• Ƙasa: India

• Harshe: Tamil

• Kasafi: ₹180 crore 

• Jimillar Kasuwanci: est. ₹285–300 crore


LABARIN SHIRIN 

Michael Rayappan shahararren ɗan daba ne da yake taimakawa talakawan yankin da yake a Chennai. Michael yana soyayya da wata likitar halittar jiki mai suna Angel Aasirvatham, wacce ta ƙi amincewa ta auri kowa sai shi, sai dai ba ta yin hakan har sai an zo dab da ɗaura auren. Akwai daɗaɗɗiyar gaba a tsakanin Michael da wani ɗan daba mai suna Daniel.

 Watarana da dare sai Daniel ya kai wa Michael da kuma babban abokinsa mai suna Kathir hari tare da yaransa. Shi kuwa Kathir, shi ne mai horas da 'yan wasan ƙwallon ƙafan mata na Tamil Nadu. A sanadin wannan hari ne dai Kathir ya samu matsala a ƙashin wuyarsa wanda ya haɗe da na bayansa, hakan ya sa zai zauna a matsayin gurgu har na shekara guda. Domin ganin cewa waɗannan 'yan mata sun samu damar shiga gasar ƙwallon ƙafa na ƙasa da za a yi a Delhi, sai Kathir ya roƙi ƙungiyar ƙwallon ƙafa na Tamil Nadu da su maye gurbinsa da Tsohon ɗan tawagarsu mai suna "Bigil" wanda ba kowa bane face Michael da kansa. 

Daga nan ne sai labarin ya juya da mu baya zuwa shekaru bakwai da suka gabata inda aka nuna mana yadda Michael ya kasance ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa wanda ya bada gudunmuwa matuƙa wajen kawowa ƙungiyar ƙwallon ƙafa na Tamil Nadu nasarori da dama shi da Kathir.
 
Mahaifin Michael wato Rayappan, ɗan daba ne da ya ke da tsohuwar gaba a tsakaninsa da Alex, wanda shi ne mahaifin Daniel. Rayappan a koda yaushe yana ƙarawa ɗansa Ƙwarin gwiwa a kan wasan ƙwallon ƙafa saboda ba ya so ya zama ɗan daba kamarsa. Yayinda Michael ya kasa samun damar shiga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasa saboda dabar da mahaifinsa Rayappan ya ke yi, sai Rayappan ya ɗauki matsalar gaba ɗaya ya kai ta ga shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta India baki ɗaya wato J. K Sharma Inda ya tilasta masa saka sunan Michael da Kathir tare da sauran 'yan tawagarsu a cikin waɗanda za a tantance. Sai dai duk da wannan ƙoƙari da Rayappan yayi haƙar Michael ba ta cimma ruwa ba sakamakon kashe masa mahaifi da Alex da Daniel suka yi a kan idonsa a ranar da zai tafi. 

Michael sai ya kashe Alex a kan idon Daniel domin ɗaukar fansar mahaifinsa. Daga nan Michael ya tsaya a Chennai ya maye gurbin mahaifinsa na shugaban 'yan dabar yankin. A yanzu kuma Michael ya karɓi roƙon Kathir da cewa zai zama mai horas da 'yan wasan don haka sai ya tafi Delhi tare da 'yan matan tare da Angel. 

Sai dai kuma 'yan matan sun ƙi bashi goyon baya a harkar wasan saboda tarihinsa na daba, hasali ma sai suka zarge shi da cewa shi ne ya jawo musu rashin nasara a wasansu na farko da Manipur, hakan ya s ma suka buƙaci hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa da ta cire musu shi. Cikin takaici, sai Michael ya miƙa takardar ajiye aikinsa ga Sharma, amma sai ya gano cewa ashe Sharma zagon ƙasa yake masa domin ya fanshe cin mutuncin da Rayappan yayi masa domin ya bashi damar shiga ƙungiyar wasa ta ƙasa. Shi ya sa ma ya aika masa da 'yan daba domin su halaka shi, amma sai Michael yayi maganinsu sannan ya janye takardar ajiye aikin nasa. 

Daga nan sai ya shawo kan 'yan matan sannan ya jajirce wajen basu horo tuƙuru da zimmar lashe gasar. Domin ya ƙara musu karsashi ma, sai ya dawo musu da wasu tsoffin 'yan wasansu biyu waɗanda ake ji da su wato Gayathri da kuma Anitha. Duk iya ƙoƙarin da Sharma yayi wajen ganin ya kawo ƙarshen tawagar abu sai ya faskara a gareshi, domin kuwa bayan sun doke tawagar Haryana daga nan sai su ka ci gaba da tafiya har sai da suka samu zuwa wasan ƙarshe wanda za a buga a Chennei kuma za su kara ne da Manipur. Ana gobe za a yi wasan ƙarshe sai aka sace ɗaya daga cikin 'yan wasan mai suna Vambu kuma Daniel ya yi mata allurar hodar iblis da ƙarfin tsiya. Ashe Sharma ne ya yo hayarsa domin ya daƙile damar su ta samun nasara, duk da cewa ta farfaɗo amma sai ya zamana ba za ta iya buga wasan ba. Ita ma jagorar tawagar wato Thendral sai aka sace ta domin a yi mata allurar, amma sai Michael ya kuɓutar da ita. Michael yayi nufin kashe Daniel amma da ya ga ɗan ƙaramin ɗansa sai ya canja ra'ayi domin ba ya so yaron ya taso da zuciyar ɗaukar fansa, hakan ya sa ya ƙyale shi. Kashegari kuwa da aka buga wasa sai ga shi tawagar Tamil Nadu ta yi nasara a bugun daga kai sai mai tsaron gida, yayin da tawagar su ka ƙaddamar da nasararsu ga kathir wanda ya zo kallon wasan a keken guragu. 

A wata nunowa ta ƙarshe an nuna yadda Michael ya ƙullawa Sharma makirci ta hanyar sanya masa hodar iblis a jaka inda aka kama shi da ita a Malaysia. Bayan wasu 'yan watanni kuma sai Michael ya aje harkar saba ya koma horas da yara wasan ƙwallon ƙafa inda har Daniel ya zo da ɗansa domin shima a koya masa sakamakon yafewa juna da suka yi. 

JARUMAN SHIRIN 


• Vijay - Michael (Bigil) da kuma Rayappan

• Nayanthara - Angel Aasirvatham

• Jackie Shroff - J. K. Sharma

• Kathir - Kathir

• Vivek - Nessi

• Daniel Balaji - Daniel

• Anandaraj - Anand

• Yogi Babu - Donald

• Arjan Bajwa - Samar

• Amritha Aiyer - Thendral

• Indhuja Ravichandran - Vembu

• Reba Monica John - Anitha

• Varsha Bollamma - Gayathri Sudharshan

• Indraja Shankar - Pandiyamma

• Gayathri Reddy - Mari

• Aadhirai Soundarajan - Minnoli

• Kanimozhi - Kanimozhi

• Shobana - Shobana

• Devadarshini - Elizabeth

• I. M. Vijayan - Alex

• Rohini - mahaifiyarsa Anitha

• G. Gnanasambandam - Aasirvatham

• Rama - Mrs. Aasirvatham

• Sai Dheena - Dheena

• Manobala - Farfesa 

• Soundararaja - Guna

• Abi Saravanan - John

• Prajuna Sarah - Mary

• T. M. Karthik 

• George Maryan 

• Mathew Varghese 

• Anish Kuruvilla 

• Sahithya Jagannathan 

• RJ Ananthi 

• Vinaya Seshan - goal keeper

• Gana Balachander 

• A. R. Rahman - Fitowa ta musamman 

• Atlee - Fitowa ta musamman 


WAƘOƘIN SHIRIN. 

1. Singappenney 
2. Verithanam
3. Unakaaga
4. Maatharey
5. "Bigil Bigil Bigiluma

Bonus Tracks

6. "Kaalame"
7. "Idharkuthaan" Dhee ,


 •----------•✬(✪)✬•----------•
 Jamilu Abdurrahman 
•----------•✬(✪)✬•----------•

    +2348185819176
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Twitter: @jamiluwriter 
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Instagram: Jamiluwriter 
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Facebook:
https://m.facebook.com/JamiluWriter/
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Tumblr: Jamiluwriter
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Bakandamiya: Jamilu Abdurrahman 
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Telegram: https://t.me/Jamiluwriter
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
LinkedIn: https://www.linkedin.com/in/jamilu-abdurrahman-36b882118
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Haimanraees@gmail.com
──────⊹⊱✫⊰⊹────── 

Post a Comment (0)