#WANDA YA RAYA DARAREN GOMAN KARSHE NA RAMADHANA YA DACE DA DAREN LAILATUL QADRI
▪الإمام ابن باز -رحمه الله-:
Yana cewa:-
*"Dukkan wanda ya raya darere guda goma na karshen watan Ramadhana, to ya dace da daren Lailatul Qadri Tabbas"*.
@الفتاوى (١٥ /٤٣٠)] .
Dan haka ga wanda yake son dacewa da wannan dare, sai ya fara ibada ta musamman tun daga yau labara da dare har zuwa daren karshen wannan watan, insha Allah ya sami daren Lailatul Qadri.
══════ ❁✿❁══════
▪الإمام عبد العزيز بن باز -رَحِمَهُ اللهُ تَعَالَى-:
Yaci gaba da cewa:-
*"Wanda ya raya waɗan nan darare yana mai imani da kwaɗayin lada, to hakika ya dace da wannan dare na Lailatul Qadri, babu shakka, kuma ya samu babban rabo daga cikin abin da Allah ya yi tanadi ga wanda ya raya wanna dare na falala da alkhairi"*.
@مجموع الفتاوى والمقالات": (١٥/٤٢٧)
Dan haka wanda yake samun Alkhairi da albarka da falalar wannan dare na Lailatul Qadri sai wanda ya hada siffofin nan guda hudu
1-Yana mai Imani wato musulmi kenan
2-Ya raya darere da kyakkyawar niyya da kwaɗayin lada a wajen Allah
3-Babu riya da Bidi'a acikin ibadar sa da waɗan nan darare
4-Sannan ya raya darere guda goma baki daya, ba wai ya ware 27 kadai ba, domin daren yana chan zawa.
══════ ❁✿❁ ══════
▪رَحِمَهُ اللهُ تَعَالَى-:
Yana cewa:-
*"Ana raya waɗan nan dararen ne da manyan ibada, Sune :-
*_Sallolin nafila_*
*_Karatun AlQurani_*
*_Azkar da Addu'a_*
*_Tuba da Istighfari da neman gafara da afuwar Allah_*
*_Sadaka da sauran aiyuakan dha’a_*
@مجموع الفتاوى والمقالات": (١٥/٤٢٦)]
══════ ❁✿❁ ══════
Allah ne Mafi sani
