*MAI TAKABA ZATA IYA FITA SALLAR IDI?*
*Tambaya*
Assalamu alaikum warahmatullah, Barka da war haka. Don Allah YA halatta me takaba ta je sallar Eid?
*Amsa*
Wa alaikum assalam,
Bai halatta ga mai takaba ba ta fita zuwa Idi, saboda Hadisin Ibnu Majah Mai lamba ta: (2031) inda Annabi SAW yake cewa da Furaia lokacin da mijinta ya Rasu: (Ki zauna a cikin gidan da kika samu labarin mutuwar mijinki har zuwa Ki kammala iddarki"
Hadisin da ya gabata yana nuna cewa: Mai takaba ba za ta fita ba sai in akwai lalura, sallar idi kuma ba ta cikin lalorori a sharia.
Imamu Ashshaukani a cikin Nailul Audaar 3/343 ya yi bayani cewa "Dukkan Mata ana fitar da su daga gidanjansu Don su halarci idi, in ban da wacce take iddar mutuwa.
Allah ne mafi Sani
*Dr, Jamilu Zarewa*
03/09/2017