GAISUWAR SALLAH

🌷 GAISUWAN SALLAH 🌷

Gaisuwan sallah ana yinta ne da kowane lafazi halastacce, lafazin da yafi falala shine *TAQABBALALLAHU MINNA WA MINKUM* domin ita ce aka ruwaito daga sahabbai.

An ruwaito daga Jubair bin Nufair yana cewa; "Sahabban Manzon (SAW) sun kasance idan suka hadu da junansu ranar idi, suna ce musu Taqabbalallahu minna wa minkum". Ibn Hajar ya hassana isnadinsa acikin Fathul baari.

An tambayi Imam Malik (Rahimahullauh) shin akwai laifi mutum ya yace ma dan uwansa bayan sallah idi, Taqabbalallahu minna wa minkum wa gafarallahu lana wa lakum, shi kuma dan uwan ya mayar masa da makamancin hakan?? Sai imam ya amsa da cewa "babu laifi hakan". Almuntaqa sharhul muwadda. 

Shaikhul islam ibn Taimiyyah yace; "Gaisuwa ranar idi, mutum yace ma ÆŠan uwansa idan ya hadu dashi bayan sallah Taqabbalallahu minna wa minkum, wa a halahullahu alaika, dama wasun irin wannan gaishe gaishen, an ruwaito su daga wani sashi na sahabban Manzon Allah, sannan wasu daga cikin imamai sun yi rangwame game da aikatashi, kamar imam Ahmad da waninsa, sai dai shi Imam Ahmad yace "Ni bazan fara yiwa kowa ba, amma idan wani yamin zan amsa masa saboda amsa gaisuwa wajibi ne" Amma fara ita wannan gaisuwar babu wata sunnah da tayi umarni da ita kamar yadda bata yi hani da ita ba, wanda yayi yana da magabata akai, wanda ma yaki yi shima yana da magabaci akai". Majmu'ul fatawa.

#Zaurenfisabilillah 

Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah

Post a Comment (0)