TAMBAYA TA 144


HUKUNCIN WACCE WANI ABU YA ZUBO DAGA GABANTA BAYAN TAYI TSARKIN JININ HAILA :

TAMBAYA TA 2751
*******************
Assalamu Alaikum malam ya ibada yau kwana hudu da gama Al adana har nayi tsarki nayi azumi yau azumi na hudu kenan na dauka. yanxu naje bayi zanyi sallan azahar sai naga wani abu dark brown ya fito to ya matsayin azumina yana nan ko ya karye ?

AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. 

Azuminki bai karye ba. Domin kuwa shi wannan brown discharge din ba'a daukarsa a bakin komai, kamar yadda Ummu Atiyyah sahabiyar Manzon Allah ï·º ta fa'da acikin wani hadisi wanda Imam Abu Dawud da Bukhariy suka ruwaito tace :

"MUN KASANCE (A ZAMANIN ANNABI ï·º) BAMU DAUKAR GURBATACCEN JINI (SHINE MAI KALAR HANTA) DA DUK WANI RAWAYA (YELLOW) A BAKIN KOMAI (IDAN SUKA ZO) A BAYAN MUNYI TSARKI".

Wato duk wani abinda ya zubo bayan sun riga sun samu tsarkinsu na haila to basu daukarsa a bakin komai. Hukuncinsa shine a wankeshi kuma a wanke duk inda ya taba. 

WALLAHU A'ALAM. 

DAGA ZAUREN FIQHU (28/09/1441 21/05/2020).
Post a Comment (0)