ILLAR RASHIN TSAFTA A GIDAJEN MATAN AURE


*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Illar Rashin Tsafta A Gidajen Matan Aure_*

Akwai abubuwan da yakamata mu lura da su, mu inganta su a wurin gina tsaftarmu. Misali wanka, wanki, wanke kai, goge dattin kunnuwa, wanke baki, wanke hannu, yankan farce, da sauransu.

A nan ina so mata su gane cewa muna da daraja da kima dole sai mun tsaya mun lura da abubuwa a cikin zamantakewar aure sannan gidanmu zai gyaru, mu kwato wa kawunanmu ‘yancinmu a hannunmu domin addinin musulunci ya fi kowane addini tausaya wa mace a tarihin dan adam.

Amma abin da ke ban mamaki sai ka shiga gidan mace ka ganshi kaca-kaca, babu sha’awa, kazanta ta tare tun daga tsakar gidanta da dakunanta da ban-daki har ita kanta. Ga tulin kayan wanki da wanke- wanke kuda suna bi ko kayan wanki a jibge, yara kuwa sai ka gan su dukun-dukun, hanci dagaje- dagaje da majina. Idan ma girki take yi sai ka gan shi a bude ko an bude murfi an bar shi a kasa ana face majina, wannan yana daga cikin abin da maza suka tsana. Kuma koma wane ne ransa ba zai so ba.

Shin ‘yar uwa ba ki san kina dasa kiyayyarki a zuciyar mijinki ba? Duk kuwa da irin soyyayar da kike ganin yana yi miki?
Wasu matan ba su dauki kwalliya da muhimmanci ba shi ya sa wasu mazan suke burin kara aure ba don ya fita ya bar ki dukun-kudun cikin dauda da tsami amma a lokacin da ya fita sai ya hadu da wata tsaleliyar budurwa tana karairaya ga shi ta caba kwalliya tana kanshi me kike tunanin zai faru, tilas ya fara saka wa a zuciyarsa zai kara aure.

Abun lura a nan shi ne, ban ce su mazan ba su da laifi ba, don a wasu lokutan za ka tarar matan ne ke da tsafta amma maigida ya kasance cikin wani irin mummunan yanayi saboda rashin tsafta. 

Amma dai abin da nake so mu lura da shi a nan mu mata mu gida ke hannunmu, duk yadda muka so sarrafa maza haka za su bi mu kamar akalar rakumi.

Duk macen da ta iya taku, ta iya kwalliya, ta iya girki, ta iya gyara gidanta ciki da waje, babu shakka za ta samun kan mijinta cikin sauki. Da zarar ya shiga gidan, ba zai yi marmarin fita ba in ba tare da wani kwawwaran dalili ba, don yana jin dadin zama a ciki. 

Ga shi gidansa ya yi fes-fes, ga uwargida ta caba kwalliya, don haka zai ji tamkar yana aljannar duniya ne.
Amma idan mace ta kasance cikin dauda, gidanta da dakinta dikin dauda, da zarar miji ya dawo to zai yi Allah-Alah ne ya bar gidan,. Wasu ba za su sake waiwayar gidan ba sai cikin tsakar dare lokacin kwanciya, kuma da zarar gari ya waye za ka ga suna hanzarin barin gidan, don wasu ko karyawa ma ba za su iya yi a cikin gidan ba saboda kazanta, sun gwammace su tafi teburin mai shayi ko dakunan cin abinci, su karya a can.

To irin wannan da me ya yi kama? Yakamama mata mu yi wa kanmu fada, mu sani igiyar aurenmu a hannunmu take, sai yadda muka so juyawa da ita. Don haka ya dace mu yi karatun ta-natsu, don mu samu zaman lafiya mai dorewa a gidajen aurenmu.

Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Sadiqqa Habib Abba*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*
Post a Comment (0)