TAMBAYA TA 83


Tambaya
:
Mene ne hukuncin irin kasuwancin nan da a ke yi wanda idan kudi hannu zaka biya Misali sai ace ka bada ₦1,000: Amma idan da kadan-kadan za ka biya zuwa wani lokaci sai ace ka bada ₦1,300. Shin mene ne hukuncin yin hakan a Shari'ance??
:
Amsa
:
Wato shidai irin wannan nau'in cinikayya shi ne Mālaman Muslunci suke Ƙiransa a lārabci da sūna:
:
           (الْـبَـيْـعُ بِـالـتَّـقْـسِـيـطِ)
:
Wato nau'in kāsuwancin da za a sayarma da HĀJA kai kuma ka riƙa biyan kuɗinta a hankali har ka gama biya, idan ya kasance kuɗi-hannu za ka biya Misāli za ka bada (₦1,000) amma idan nan gaba ne za ka biya da kaɗan-Kaɗan to za ka bada (₦1,200) ne:
:
Mālamai sunyi saɓānī game da hukuncin irin wannan nau'i na kāsuwanci, waɗansu 'Yan-kaɗan daga cikin Mālamai kai tsaye sukace bai halatta ba saboda a ganinsu yin hakan kamar akwai riba a cikinsa sakamakon ƙārin da a kayi a ciki, sai dai mafi yawan Mālamai sukace hakan ya halatta tun da yarjejeniya ce a kayi kuma kowa yā yarda da hakan, Mālaman da sukace ya halatta sun kafa hujjar su ne da faɗin Aʟʟαн(ﷻ) inda Ya ke cewa:
:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَأْكُلُوا أَمْوَالَكُم بَيْنَكُم بِالْبَاطِلِ إِلَّا أَن تَكُونَ تِجَارَةً عَن تَرَاضٍ مِّنكُمْۚ…… (البقرة-29)
MA'ANA:
Yā kū waɗanda ku ka yi īmāni, kada kuci dukiyarku a tsakanin ku ta hanyar ɓarna (haram), sai dai in ta hanyar wani kāsuwanci da ku ka ƙulla ne tare da yarjejeniya atsakāninku……
:
Sannan waɗannan Mālamai sukace Nassi yā tabbata a kan halaccin yin kāsuwanci amma a yi jinkirin bada kuɗi, kamar yadda suka kafa hujja da Hadisin Sahīhul-Bukhāri wanda ke cewa:
:
''وعن عائشة رضي الله عنها قالت : جاءتني بريرة . فقالت : إني كاتبت أهلي على تسع أواق ، في كل عام أوقية''……
MA'ANA:
Daga A'isha Aʟʟαн(ﷻ) ya kara yarda a gare ta: ta ke cewa, Barīrā (wata baiwa ce) ta zo gareni tace dani iyayen gidana (waɗanda suke mallakata) sun rubuta mini kuɗin fansa a kan Ūƙiyya-9 da zan biya na fanshi kaina, (zan riƙa biya da Kaɗan-Kaɗan) kowacce shekara zan bada Ūƙiyya-1:
:
Danhka sukace wannan dalili ne a kan halaccin kāsuwanci da kuma jinkirin biyan kuɗi, to amma sai dai dukkan waɗannan Nassosi da a ka kawo babu inda a kayi maganar yin kārin-kuɗi a cikinsu sakamakon jinkirin da akasamu, wanda kuma wannan gaɓa itace Muhallin-saɓānīn, wannan tasa wasu Mālamai suke ganin cewa wannan Ƙārin-Kuɗin da a kayi a matsayin riba yake, to amma gaskiya mafi rinjayen Mālamai duk sun tafi ne a kan halaccin irin wannan nau'i na kāsuwanci, cikinsu harda Mazhabobinnan guda-4 sanannu, wato: Mālikiyya, Shāfi'iyya, Hanafiyya, Hanābil, Kuma duk sunkafa hujjar su ne da faɗin Aʟʟαн(ﷻ):
:
وَأَحَلَّ اللَّهُ البَيعَ....... (سورة البقرة 275)
MA'ANA:
Aʟʟαн(ﷻ) Yā halatta Kāsuwanci………
:
Da kuma Hadisin da ke cikin Sahīhul-Bukhāri wanda yake cewa:
:
قَدِمَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهم عَلَيْهِ وَسَلَّمَ الْمَدِينَةَ وَهُمْ يُسْلِفُونَ فِي الثِّمَارِ السَّنَتَيْنِ وَالثَّلَاثَ……
MA'ANA:
Mαиzoи Aʟʟαн(ﷺ) Yāzo ya samu mutanen MADĪNA su na yin (nau'in cinikayyar) kayan amfanin gōna tare da jinkirin biyan Kuɗin har zuwa shekara-1 ko-2……
:
Danhaka dai a bisa ga zancen da yafi rinjaye a wajen Mālamai shi ne: irin wannan nau'i na cinikayya ya halatta, kamar yadda mafi yawan Mālamai suke bayar da fatawa akan hakan:
:
※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
:
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
              Daga Zaυren
             Fιƙ-нυl-Iвadaт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
           Mυѕтαρнα Uѕмαи
              08032531505
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Post a Comment (0)