TAMBAYA TA 84


Tambaya
:
Menene hukuncin neman auren da'akayishi alhali mace tana cikin idda, kokuma akadaura auren batagama iddaba??
:
Amsa:
:
Dukkan Malamai Ma'abota ilimi sunyi ITTIFAƘI akan cewa iddar Mace dai bata wuce ɗaya daga cikin halayennan guda uku:
:
1-Kodai yakasance ma'abociyar al-adace, to iddar irin wannan yazama zatayi jini uku kenan, Saboda fadin Allah(ﷻ):
:
والمطلقات يتربصن بأنفسهن ثلاثة قروء (البقرة/228)
Ma'ana:
(Matan da) akasakesu zasu zaunane harsuyi Jini uku (tsarki uku)
:
2-Idan kuma ta kasance batayin al'ada saboda tsufa kokuma ƙuruciya, to iddarta zatayi watanni uku ne, kamar yadda Allah(ﷻ) yafada:
:
واللائي يئسن من المحيض من نسائكم إن ارتبتم فعدتهن ثلاثة أشهر (الطلاق/4)
:
3-Idan kuma mai ciki ce to iddarta shine tahaife abindake cikinta kawai, kamar yadda Allah(ﷻ) yafada:
:
وأولات الأحمال أجلهن أن يضعن حملهن، (الطلاق/4)
Ma'ana:
Ma'abota ɗauke da ciki (juna biyu) iddarsu shine suhaife abindake cikinsu,
:
Danhaka shidai neman aure acikin idda kodai mutum yafito fili ƙarara yayi kamar yace da mace idan kingama idda inasonki zan aureki, koyaje wajen waliyyinta yagaya masa cewa zai aureta, to wannan haramunne bai halattaba, Sannan kuma akwai jirwaye me kamar wanka, wato mutum yanuna alamun yanaso amma baifito fili ƙarara ya bayyanaba, kamar taga haka kawai ya aikomata dawata kyauta maitsoka, kokuma yace mata nikuwa inason shawara dake idan kingama idda, dadai sauran makamancin haka, to irin wannan babu laifi ayi, amma da sharadin yakasance iddar tata ba ta kome bace, amma idan iddar komece to shima bai halattaba, domin idan mace tana cikin iddar kome hukuncita na matar aurene kuma baya halatta anemi matar aure alhali da igiyar auren wani akanta.
:
Danhaka idan Mutum yanemi auren mace kafin tagama idda amma ba'a kaiga ɗaura musu aurenba saida bayan tagama idda, dayawa Malamai sukace auren yayi, amma an aikata haramun awajen neman auren, danhaka wajibine su tuba ga Allah(ﷻ) akan wannan laifi dasukayi, amma idan yakasance anɗaura aure kafin mace tagama idda amma mijin bai kaiga saduwa da'itaba, to dama asali wannan auren ɓataccene, danhaka za'araba wannan aurene har sai taje taƙarasa wannan iddar tata sannan azo asake sabon ɗaurin aure, domin baya halatta aɗaura aure acikin idda kuma koda wacce irin iddace mace takeyi, saboda Faɗin Allah(ﷻ):
:
ولا تعزموا عقدة النكاح حتي يبلغ الكتاب أجله.
:
Amma idan akaɗaura aure acikin idda kuma mijin yasadu da Matar to bayan anraba auren zatayi idda ne har guda biyu, tafarko zata ƙarasa cikon iddarta ta mijin farko sannan kuma tasakeyin idda ta miji nabiyu, Sannan Mazhabin MALIKIYYA dawani sashe na Mazhabin HANABILA sukace har-abada babu aure atsakinsu tunda ya aureta kuma yasadu da'ita cikin idda, saidai mafi yawan Malaman Mazhabin SHAFI'IYYA, da HANAFIYYA dakuma HANABILA, sukace ya halatta yasake aurenta bayan taƙarasa iddar farko, amma Mazhabin HANABILA sukace kafin ya aureta sharaɗine sai bayan taƙarasa iddar mijinta nafarko dakuma iddarsa, amma maganarda mafi yawan Malamai suka rinjayar itace, ya halatta yasake aurenta bayan taƙarasa iddar mijinta nafarko, sukace babu buƙatar wai shima saitayi masa idda kafin yasake aurenta.
:
※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
:
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
              Daga Zaυren
             Fιƙ-нυl-Iвadaт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
           Mυѕтαρнα Uѕмαи
              08032531505
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Post a Comment (0)