TSAKANIN MU DUK DA BANBANCINMU 1


*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//01๐Ÿ“ฟ*

*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*

Godiya ta tabbata ga Allah mahaliccin kowa da komai, wanda ya qagi halittan dan adam daga rashi, ya yawaita halittar kuma ya sanya mu'amalla a tsakanimmu ta zama rukuni na rayuwa da ibada, tsarki ya tabbata ga maliccin kowa da komai, sai kuma salati da sallama ga fiyayyen halittar Muhammad SAW.

Haqiqa mu 'yan adam rayuwarmu ta faro ne tun daga adam AS, sai ta riqa samun ci gaba ta wurin kwashe 'yan baya ana yin sabon zubi a duk lokacin da al'ummar ta lalace, sai dai daga Annabi SAW ba a sake kwashe al'umma gaba daya a dalilin sabo ba, wasu kan mutu wasu na raye, ko dai rayuwar magabatansu ta zama musu izina su gyara halayensu, ko kuma su ci gaba da zama cikin batan basira da sabo har wata uquba daga Allah SW ta sake gangaro musu ta dibi na diba ta qara gaba.

Mu dai a wannan lokaci da muke ciki wasu abubuwa na hatsari na kewaye damu wadanda sai 'yan qalilan ne suke iya karantawa su san abinda muke ciki, ko in sun gane su gyara ko su qyale, daga cikin abubuwan akwai:-

1) Raunin da jama'armu suka sami kansu a ciki ta bangaren addini, siyasa, kasuwanci, rayuwa, kai har da dabi'u na qwarai da tarbiya da sauransu.

2) Yadda al'umma suka sami kansu a zaman marina, ko kuma karkasuwa zuwa qasashe wadanda muminai suka sami kansu a qasar da tsarin mulkin bin abinda shari'a ta tanadar, ko kuma a qasa guda amma muminai na bin sarkunan da ba a qarqashin sarki guda suke ba, kowa cin gashin kansa yake, ba mai saka shi ko ya hana.

3) Yadda mutane suka karkasu zuwa mazahabobi ko qungiyoyi na addini, wannan ya ce abu kaza ba kyau wannan ya ce a mazahabarsa ko qungiyar da yake bi daidai ne.

4) Yadda ainihin masu koyi da ayoyi ko hadisai suka sami kansu a yau, idon kowa a kansu ne yana qoqarin ganin bayansu, su kuma sun gaza samun matsaya da za su tausaya wa junansu kamar yadda sahabban manzon tsira suka yi.

5) Samun wasu bangarori da suke janyo wasu addinai jiki, har ma su yi musayar fahimta ko yarjejeniya ko tarukan addini don dai kawai su sami fahimtar juna ko taimako a kan 'yan uwansu na addini dalilin wani dan sabani dake tsakaninsu.

6) Tsari na abokan gaba don tarwatsa wannan al'umma ta hanyoyi daban-daban, masamman yadda al'ummar za ta koma yaqi da juna, da kashe-kashe tsakaninsu ba tare da su abokan gaban sun shiga ciki kai tsaye ba.

7) Yadda muka sami kammu a yau na kowa malam, sai sabbin fatawoyi wadanda duk an san sun ci karo da koyarwar ma'aiki, da qin bin hanyar da malaman farko wadanda suka yi karatu gun malaman gaskiya.

8) Ga yada barna ta hanyar kafofin sadarwa, ko yawo bude idanu yadda wasu al'adu da ba mu san su ba suka shigo.

9) Da yadda ake tunzuro talakawa don su yi wa shugabanni bore da gangan, a kuma sa shugabannin su qi tausaya wa talakawan, kodai saboda abinda suka yi ko wata manufa ta daban.

10) Sanya sabani ko rashin fahimta a tsakanin rukunnan jama'a, kamar uwaye da diyoyinsu, ko mata da mazansu (misali a ce mata ba bayi ba ne, ko in namiji ya mare su su rama da dai sauransu), ko a ce wata jama'a tana danne wata, ko zancen neman sarauta ko wani matsayi a hukumance da dai sauransu.

11) Dago fituntunu a tsakanin qungiyoyin addini (Kamar Qadiriyya da Tujjaniyya, Dariqa da Izala, Salafiyya da Shi'a da dai sauransu).

Wadannan matsaloli ba qanana ba ne, suna buqatar malamai, masamman wadanda suka hada ilimin addini da sanin zamantakewa, da su sake nazari kan yadda rayuwar al'umma ta yi qamari a yau, su fara nemo mafita in har hakan zai samu, ba yadda za a yi ci-gaba ya sami matsuguni a tsakankanin jama'a matuqar suna da yamutsi da tashin hankali a tsakaninsu, koda ba a iya magance matsalolin ba, a samo wata mafita da za ta ba da daidaituwa wurin zaman tare duk da sabanin dake tsakankanin juna kamar dai yadda muke tare a da.

Zamuci gaba insha Allah.


*Gabatarwa: Abulfawzhaan*
Post a Comment (0)