TSAKANIN MU DUK DA BANBANCINMU 18


*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//18📿*

*GINSHIQI NA SHA SHIDA*

*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*

KARE MUTUNCIN MUSULMI

Kare mutuncin musulmi abu ne dake rubuce a Qur'ani da Hadisi da maganganun malamai, shi ya sa ya zama wajibi ga dukkan musulmi, kar a keta masa mutuncinsa a kan wata 'yar qanqanuwar shubuha, ko don wani sabani da bai taka kara ya karya ba, to bare kuma a dubi malami wanda duk yankin an yarda da iliminsa sai wani dalibi da bai jima da fara karatu ba ya ce masa jahili, ko dan bidi'a cikin sauqi ba tare da ya damu ba, tabbas Qur'ani ya tabbatar da haramcin jinin musulmi, ko mutuncinsa ko dukiyarsa, wannan kawai ya isa.

Me da me ya kula kafin ya tabbatar da cewa jahili ko dan bidi'a? Kai duk wani wanda ba a tabbatar da laifinsa ba koda kuwa arne ne, Allah SW yake cewa ((Wadanda kuka yi imani in wani maikuskure ya zo muku da magana ku tabbatar tukun don kar ku abka wa jama'a kan rashin sani ku dawo kuna nadama a kai)) Hujraat 6, anan Allah SW ya sanya sharadin tabbatar da abinda ake zargi tukun, don kar a far wa wanda ake zargin daga baya a zo ba haka ba ne lamarin ya rincabe, anan fa kowa na iya shiga, mutumin qwarai ne ake tuhuma ko mutumin banza, kar daga an ce wane ya yi kaza ko ya ce kaza ka ce "Wallahi har qimarsa ta zube a idona, ban ganinsa da wani mutunci ko kadan, ashe dan bidi'a ne!".

Allah SW ya sake fadi a ayar dai, ya ce ((Ku da kuka yi imani kar fa wata jama'a ta yi wa wata isgili, qila wace ake yi wa isgilin ta fi ta nagarta, kar wasu mata su yi wa wasu matan sai wadanda ake yi musu din su fi su inganci, kar ku baci junanku, kar ku riqa jifar juna da muggan laqabobi, tir da sunan fasiqanci bayan imani, duk wanda bai tuba ba wadannan kam azzalumai ne. Ku da kuka yi imani ku nisanci yawan zace-zace, wasu zace-zacen zunubi ne, banda binciken qwaqwab, banda gulman juna, dayanku zai so ya ci naman gawar dan uwansa? Ai kun qi haka ko? To ku ji tsoron Allah, lallai Allah mai yawan karbar tuba ne mai yawan jinqai)) Hujraat 11-12.

Duk da nau'in ayyukan barnan da Allah SW ya ja kunnuwanmu a kai munana ne, da zai tsoratar da mu kalli yadda ya bude maganar ((Ku da kuka yi imani!)), a hadisai kuwa ga wani da Abu-Huraira RA yake cewa Annabi SAW ya ce: " Kar ku yi wa juna hassada, kar ku shiga ciniki don ku ingiza wani ya fada ba saya za ku yi ba, kar ku yi qiyayya, kar ku juya wa juna baya, kar wani ya yi ciniki kan cinikin dan uwansa, ku zama 'yan uwa bayin Allah..."

"... Musulmi dan uwan musulmi ne, bai cutarsa bai qasqanta shi, bai tozarta shi tsoron Allah anan yake (Ya fadi har sau uku yana nuna qirjinsa) musulmi ya tozarta dan uwansa ya ishe shi bala'i, duk wani musulmi jinin dan uwansa haramun ne a kansa, haka dukiyarsa da mutuncinsa (Muslim 6493). Ibni Taimiya yake cewa "Asali jinanen musulmi da dukiyoyinsu da mutuncinsu haramun ne a tsakaninsu ba su halasta sai da izinin Allah da manzonsa".

Ya ce "Zai yuwu wadanda suka san haramcin hakan su wuce gona da iri ga masu tawili, su zarge su a kan wani abinda Allah ma zai yi musu gafara, sai daga baya kuma wasu su zo su qara wanda ya fi wancan, su shiga har cikin mutuncin 'yan uwansu, wanda Allah ya haramta hakan da manzonsa (Al-Istiqama 1/301-302), Shaukani yake cewa "Ka sani mun gabatar cewa Allah ya haramta yi da wani, wannan tabbatacce ne a Qur'ani da Sunna da fahimtar malamai, akwai maganar ta sigogi daban-daban a Qur'ani da Sunna wadanda suka tattaro gamayyan haramcin yi da wani ga dukan musulmi.

Bai yuwuwa a ce akwai wani wuri da ya halasta banda wani, ko wani ya haramta masa banda wani sai in akwai hujjar da ta kebance hakan, in an sami hujjar shikenan, in ba a samu ba to fa kamar liqa wa Allah ne zance, da halasta abinda Allah ya haramta ba tare da dalili ba (Raf'ur reeba 1/50) Ibn Taimiya ya ce "Abin mamaki za ka ga mutum cikin sauqi ya iya tsare kansa ga cin haram, zalunci, zina, sata, shan giya, kallon haramci da sauransu, amma ya kasa tsare harshensa, da yawa za ka ga mutum mai tsantseni ya nisanci alfahasha da zalunci amma harshensa bai qyale mutuncin rayayyu ba bare matattu, bai damu da abinda zai fada ba (Ad-Da'u wad dawa p187).

Mutuncin musulmi tsararre ne, bai halasta ba a fitar da shi daga muslunci in ba da qwaqqwarar hujja ba Buhari ya rawaito, a hadisin Buhari Annabi SAW ya ce "Wani bai jifar wani da fasiqanci ko da kafurci sai ya dawo masa in abinda ya zarge shi da shi ba haka ba ne (Buhari 6045) a ruwayar Muslim ya ce "Duk wanda ya jingina wa wani kafurci ko ya ce masa abokin gaban Allah alhali ba haka ba ne sai ya abka ciki (Muslim 61), mu ji tsoron Allah kan kalmominmu masamman a wuraren koyarwa, in ka sami kanka a matsayin malami abinda za ka fadi kadan ne, dalibanka ne za su kwasa su qara nasu su watsa a gari, Allah ya yi mana tsari.

Zamuci gaba insha Allah.

*Gabatarwa: Abulfawzhaan*

*Follow my Facebook page*
https://www.facebook.com/100625758324355?referrer=whatsapp
Post a Comment (0)