TSAKANIN MU DUK DA BANBANCINMU 24


*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//24📿*

*GINSHIQI NA 22*

*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*

BANDA CEWA "SAI WANE"

Idan ana son a lalubi gaskiya to fa in ba Shari'a ba bai dace ba a ce sai dai maganar wane, muna sane da cewa akwai bambancin maganganun malamai da yawa a mas'alolin addini da dama, wannan kuwa kan faru ne a dalilin bambancin da ake samu wurin hangen nesa, da fahimta, da hanyoyin da ake bi wurin tsakuro hukunci da sabanin da ake samu wurin fahimtar wata hujja da za a kafa, wannan ya sa aka sami nau'o'i da dama wurin fatawa, wani sa'in ma su yi hannun riga da juna, duk da haka za ka taras kowani malami yana da almajirai da dama masu daukar karatu a qarqashinsa ko masu bin fahimtarsa.

Ko ya aka yi dai irin wannan fatawoyin bai dace ba a ce sun zama dalilin da za a saba da juna, al'umma ta rarraba, ko su zama dalilin da mutum zai ce "Ni fa karatun malam wane kawai, ba ruwana da sauran malaman!" Dalili kowa qoqarinsa kawai yake yi a matsayinsa na dan adam, zai iya yin daidai ko kuskure, ba wanda za a ce abinda ya fadi dinnan yanke shi ne manufar Allah SW, sai dai ana kyautata zaton haka, domin da mun sakankance cewa maganar wane yanke ita ce daidai, to duk wace ta saba masa ta zama kuskure kenan.

Bisa wannan dalilin zantukan wani malami ba a daukarsu a matsayin shari'a, bare har a ce su kadai kawai za a bi, misali ka ce "Ni mazahabar Maliki kawai, ko Shafi'i zan bi" ko ka ambato sauran, duk wani masani tunda ba Allah SW ba ne, ba kuma manzon da ya turo ba ne, zai iya yin daidai kuma zai iya yin kuskure, to in aka yi dace da kuskuren kuma ka ce shi din kawai za a bi fa? 

In dai ya yi magana ta dace da Qur'ani ko Sunnar ma'aiki, to a wannan lokaci karkatar za ta kasance ne ga Qur'ani ko Sunna ba wai malamin ba, malamai na da buqatar a girmama su, a dauki koyarsu, a yi musu ladabi, amma a ajiye su a mazaunansu, kar a kai su inda Allah SW bai kai su ba, asali ma tsayawa a koyarwar malam wane yakan kai ga rabuwar kan al'umma tunda kowa da malaminsa, amma in aka tsaya kan Qur'ani da Sunnar Annabi SAW wannan zai ma hada kan al'umma ne, tunda kowa ya yarda da cewa su ne farko, kuma su ne tushe.

Ibn Taimiya yake cewa "Duk wanda ya wajabta yin koyi ga wanda ba manzon Allah ba a kan duk abinda ya yi umurni da shi, to fa ya wajabta gasgata shi a kan duk abinda ya fadi, ya tabbatar da cewa ba ya kuskure, ko liqa kiyayewarsa da duk abinda yake umurni da shi a cikin addini, a haka ya sanya shi daidai kenan da manzon Allah SW, saboda kebantattun abubuwa na manzanci da ya liqa masa, koda kuwa wadanda ya ba wa wadannan sifofin wasu sahabbai ne, ko makusantan Annabi SAW, ko wasu shugabanni, ko shehunnai, ko sarakuna da sauransu (Jami'ur Rasa'il 1/273).

Da wannan za mu fahimci bai dace ba sam a ce sai dai fahimtar malam wane, ta yadda za a qaurace wa waninsa koda kuwa malamin da aka zaba ne ke kan kuskure, shi kuma wanda aka ya wofintar shi ne a kan hanyar daidai, yin hakan na nuna an tabbatar da cewa malamin da aka zaba ba ya kuskure, malaman duniya kab dinsu matuqar sun tsaya kan koyarwar Qur'ani da Sunnar Annabi SAW, da fahimtar magabata na qwarai duk malamanmu ne, a ko'ina suke kuwa, ya kasance cewa manufar musulmi ita ce bin duk wata magana da aka iya kawo hujja ta shari'a a kai, ba kame-kamen wani ba.

'Yan Shi'a sun ba malamansu da wadanda suke ganin cewa salihan bayi ne wadannan sifofi, shi ya sa za su kira dayansu su ce masa Alaihis salam (AS), wato kamar dai yadda ake kiran manzanni, wannan sun fito qarara sun fadi ba zagaye-zagaye, cewa su ga manufarsu, wanda zai fahimta ya fahimta, wasu kuma ba za su iya yin hakan ba, sai suka riqa ce wa zababbunsu Radiyal Lahu anhum (RA) kamar yadda ake ce wa sahabbai, sun kai su wancan matsayin, muna sanin cewa sahabbai dukkansu masu adalci ne a maganganunsu da ayyukansu, kenan su ma ba za su saki maganganun zababbunsu ba don ga matsayinsu, asalin sakin hanyar da muka sami kanmu a yau kenan.

Zamuci gaba insha Allah.

*Gabatarwa: Abulfawzhaan*

*Follow my Facebook page*
https://www.facebook.com/100625758324355?referrer=whatsapp
Post a Comment (0)