LAILATUL QADR 4

🌺 *LAILATUL QADR 4*

WANA IRIN IBADAH AKAFISO ACIKIN WANNAN DAREN??

🔶 Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama yana cewa "duk wanda ya tsaya acikin daren lailatul qadr yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abunda ya gabatar na zunubansa". Tsayuwar daren kuwa shine rayashi da tahajjud da salloli.
  Sannan kuma fiyayyen halitta ya umarci Nana Aisha Allah ya kara mata yarda da ta yawaita addu'a acikin wannan daren. 
    Wannan yasa Sufyan As-Sauri Allah ya masa rahama yake cewa "Yin addua acikin wannan daren shiyafi soyuwa agareni samada yawaita sallah, amma idan zai hada sallah da adduan hakan shiyafi", saboda Manzon Allah ya kasance yana sallah acikin wadannan dararraki, Sannan yana karatun Alqurani tartilan acikin sallarsa, babu wata aya ta rahama da zai iso face ya roki rahama, hakan idan yazo kan ta azaba sai ya nemi tsari. Kaga kenan ya hada tsakanin sallah da karatun Alqurani da kuma Addua.
  🔸 Addu'ar da manzon Allah ya karantar da Nana Aisha tana fadi acikin wannan wata shine;
اللهم إنك عفو تحب العفو فاعف عني

#zaurenfisabilillah
https://t.me/Fisabilillaaah

Post a Comment (0)