ƘOFAR ADDU'A KENAN

🌗 *KOFAR ADDU'A KENAN* 🌗

Sau uku ake Kwankwasa kowace irin kofa, idan kaji shiru sai ka juya katafi abinka, inbanda *Kofar Addu'a* ita kadaice ba'a gajiya da kwankwasawa, kayi tayi yadda Addini yace kayi, banda tsallen badake, har ka koma ga Allah. 

Ita *kofar Addu'a* dabam take da sauran kofofi, abude take amma ba kamar yadda zamuyi tsammani ba, kuma ana kwankwasata ne da ladabi, hakuri da juriya, kada kayi mata gaugawar kamar kace: 

"Kai kana ta kwankwasawa amma har yanzu shiru anki budewa," Dan uwa, Kasanya a ranka cewar za'a bude nan ba da jimawa ba, kayi yaqinin kamar ma anbude ne kuma maka, lokaci kawai kake jira. 

Ko kasan cewa : 'Ya'Yan itatuwan Bishiyar da ba ta saurin girma, galibi sune sukafi daraja da qima, kuma idan aka dandana su za'aga sunfi dadin dandano. 

Mafi yawan lokuta jinkirin biyamaka abinda ka roka Alkahairi ne, amma sai idan anyi hakuri kuma aka kyautata wa Allah zato, Sai kaga ta bayar da kyau doriya bisa abinda ake sa mata ran tayi. 

Ya Allah ka karba mana ibadunmu kuma kabiya mana bukatunmu na Alkhairi, ja bamu kyakkyawa anan duniya da lahira, ka tseratar da mu daga shiga wuta kuma kasanya mu cikin Aljannah da rahamarka. 

✍🏻 *Idris M Rismawy*
Rismawy86@gmail.com

Post a Comment (0)