TSAKANIN MU DUK DA BANBANCINMU 5


*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//05📿*

*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*

GINSHIQI NA BIYU

*BANDA KODA KAI*

Ba ina zargi ba ne ko kushe, ina ganin kamar in gora ya cika duk yadda ka girgiza shi ba ya qara, babu buqatar ka yi ta kwazazanta kanka da fadin tarin iliminka, mutane na neman ilimin ne ba tarihinka ba, wani ko gabatar da dan wani abu zai yi sai an hasko shi da tarin littafai a ma'ajiyarsa, za ka ga manyan malaman suna da ukun wadannan ko fiye amma in ba karatu suke ba ba za ka gan su da ko littafi daya ba, in dai mutum na da sani to a gan shi a wurin koyarwa, da kuma yadda yake ma'amalla da dalibansa da sauran jama'a.

Malam in wani daga cikin almajirai 'yan uwanka ya saba maka wurin fahimtar wani nassi to ko hukuncin wata matsala bai dace ba koyaushe ka riqa ganin kai ne gasgiya fahimtarka ita ce daidai wace sam ba ta garwaya da kuskure ba, shi kuma abokin jidalin naka shi ne mai kuskure kuma sam babu gaskiya a maganarsa, zahiri wannan ba wai rashin adalci ne kawai ba, akwai ma nau'i na wanke kai, da alfahari da sani, ko alfahari da malamin da kake kafa hujja da shi, adalci anan in ka fahimci lallai akwai wani kuskure ko qarami ne a maganarka ka fito da shi, kuma in ka tsinci daidai a maganarsa ka tabbatar da shi.

Masamman kasancewar mutum bai da wani dalili da zai tabbatar na cewa lallai shi ne mai gaskiya, wancan ne mai kuskuren, Mai sharhin littafin (Al-Ashbaah wan-Naza'ir) yake cewa: "In aka tambaye mu kan mazahabarmu ko wadanda muka saba da su a fiqihu ya zama dole mu ba da amsar cewa: Mazahabarmu ce daidai amma za a iya samun kuskure, su kuma wadanda suka saba mana mazahabarsu kuskure ce amma za a iya samun daidai a ciki, domin in muka yanke magana guda tabbas kuskure ne, duk wani mai ijtihadi zai iya yin daidai kuma zai iya yin kuskure, don tambayar in an yi za mu ce mazahabarmu ce daidai tasu kuma kuskure ce (Gamzul Uyunil Basa'ir 7/262).

Wannan kusan mu ce mazahaba ce ta masu falsafa, su kam sukan daga qafa a fiqihu, sai su tsananta a lamuran aqida, ba shakka wannan ya saba mazahabar magabata, don su sukan yi wa mutum hanzari a kowani irin lamari, fiqihu ne ko aqida, domin lokacin da Allah SW ya koyar da mu yadda za mu ce (Ubangijimmu kar ka kama mu in mun yi mantuwa ko kuskure) ya ce "Na ji" (Ad-Dawabitul Fiqihiyya p26 Ahmad bn Sa'ad Hamdani Al-Gamidi)

GINSHIQI NA UKU

*SANYA WA ZUCIYA KARBAR GASKIYA*

Idan aka sami sabani wurin fahimtar nassi ko hukuncin wata matsala ta addini za ka taras fahimtar kowa ta saba juna, ko ya kasance wannan ya inganta hukuncin wata matsala wace wancan bai inganta ta ba, a irin wannan lokacin ko dai dukansu biyun suna kan kuskure, ko kuma duk sun yi daidai, ko daya ya yi daidai daya ya yi kuskure, ko a sami daya ya yi daidai ta wata fuskar ya yi kuskure ta dayar, illa-iyaka, mu kam a mazahabar ahlus sunna ba yadda za a ce kiyoshin abu duka daidai ne.

Don kowace mas'ala akwai hukuncinta a shar'ance, ba za a ce mas'alar da daya ke warware daya duk daidai ne ba, amma kamar sauran ukun tabbas za a iya samun matsaya, to a irin wannan lamari in suka binciki wata matsala a qarshe ya bayyana cewa abinda wani ya tafi a kai shi ne daidai to ya zama dole dayan ya karba, ya dawo daga fahimtarsa, shi kuma wanda aka karbi nasan ya taimaki mai kuskuren ta yadda ba zai canja ra'ayi ba, misali kar ya nemi qasqanta shi.

Don mutum a dabi'arsa yana ganin shi yake da gaskiya matuqar bai koma fahimtar wanda suke tattaunawa tare ba, to idan ya bayyana masa cewa shi yake da kuskure to ya zama masa dole ya canza ra'ayi, wannan wani matsayi ne da ba kowa ke samunsa ba sai jaruman da suka fi qarfin suciyarsu, daga cikin abinda Al-Gazali ya kawo dangane da Hatimul Asum ya ce "Ina da abubuwa uku dake tsakanina da wanda muke muhawara da shi: Nakan nuna jin dadina in ya yi nasara a kaina, nakan damu in ya gaza, nakan yi qoqarin kare kaina kar na yi masa ahinda zai dame shi" da wannan maganar ta kai ga Imam Ahmad sai ya ce "Subhanallah, in dai game da hankali ne ban hada shi da kowa"

Gazali ya ce "Da dayanku yana tauna-tauna da wani ka dubi fuskarsa, in gaskiya ta bayyana ga abokin tauna-taunar, ka dubi yadda yake qoqarin kunyata shi, da yadda yake aiki da duk abinda yake da shi wajen jayayya, ko yadda zai yi ta kushe abokin jayayyar tsawon rayuwarsa" don haka ya sa sharadin cewa dole mai tauna-tauna "Ya zama kamar mai cigiya, zai dai sanar amma bai damu a gani a hannunsa ko a hannun wani ba (Ihya'u Ulumuddeen 1/64).

Shafi'i yake cewa " Ban taba tauna-tauna da wani ba sai na yi addu'ar cewa: Allah ka sanya gaskiya a zuciyarsa da bakinsa, in ni ke da gaskiya ya bi ni, in kuma shi ke da ita na bi shi (Qawa'idul Ahkam 2/136)

Zamuci gaba insha Allah.

*Gabatarwa: Abulfawzhaan*
Post a Comment (0)