*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//20📿*
*GINSHIQI NA SHA TAKWAS*
*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*
KUSKUREN DA MUTUM KAN SAMU BA YA NUFIN YA SAKI ALLAH
A muslunci akwai wani tsari na shari'a wanda wata alaqa ta addini ta harhado mutane wuri guda, wannan alaqar ce Allah SW ya kira ta da 'yan uwantaka, wato duk wani musulmi dan uwan musulmi ne, koda kuwa daya musulmin mai sabo ne, fasiqi, wannan sabon ba ya yanke wannan alaqar ta addini, kai ko dan bidi'a ne matuqar bidi'ar ba ta kai shi zuwa ga kafurci na zahiri ba, wannan gamayya da Allah SW ya yi mana gamayya ce ta imani da ya kamata kowani musulmi ya kula da ita.
Allah SW yana fadi a Qur'ani cewa ((Muminai 'yan uwan juna ne ku inganta tsakaninku, ku ji tsoron Allah, lallai zai yi muku rahama. Al-Hujraat 10)), da wannan Annabi SAW yake cewa "Dayanku bai zama mumini sai ya so wa dan uwansa abinda yake so wa kansa (Buhari 178), kar ya zama burinka a kullum ya za ka zaqulo dan uwanka mumini ka cillar da shi waje ta hanyar kafurta shi, ka muzanta shi ta wurin bidi'antar da shi ko fasiqanta shi, wadanda suka yi imani sukan matsa wa kafurai ne amma sukan tausasa a tsakaninsu.
Ibns Salah yake cewa "Imanin dayanku bai cika sai ya so wa dan uwansa a muslunci abinda yake so wa kansa, ya sami abinda shi ma ya samu, ya ni'imtu da wata ni'ima kamar tasa ba tare da ya tauye masa komai ba, wannan abu ne mai sauqi ga wanda yake da lafiyayyar zuciya, wanda ke da wani qulli ne a zuciyarsa yake ganin wahalar hakan, Allah SW ya ba mu lafiya mu da duk 'yan uwanmu gaba daya (Sharhin Nawawi na Muslim 2/17).
Wanda duk yake so wa dan uwansa alheri yake qin mummunan abu ya same shi da wahala ka ga ya cutar da shi, ko ya yi masa fatar mummunan abu, amaimakon haka sai dai ya qaunace shi, ya riqa yaba masa da alkhairi a kowani lokaci, wannan yana cikin imani, sai dai wannan fa ba ya nufin cewa in ya yi kuskure ba zai nuna masa kuskurensa ya yi masa nasiha ba, ba sharadin 'yan uwantakar da aka ambata a baya ne ba a ce mutum ba zai yi sabo ko ya aikata bidi'a ba, sai dai matsayinsa ya yi rauni a dalilin abinda ya aikata, amma 'yan uwantakar tananan.
Ba za ka gudu ka bar shi cikin halaka ba, yanzu ne ma ya kamata ka nuna kai dan uwa ne na qwarai ta wurin lalubo hanyar da za ka tsamo shi daga halakar da ya shiga, a maimakon ka ruga ka bar shi, kuskuren da mutum zai samu a wurin malanta kuwa bai nufin shikenan ya sami matsala a tsakaninsa da sauran 'yan uwansa musulmai, ai ijtihadi ya yi, mun kuma karanta hukuncinsa a baya, har ma mun ga matsayin da Allah SW ya ajiye shi.
Yadda Allah SW ya fadi a harshen Annabi SAW ya ce ((Ubangiji kar ka kama mu in mun yi mantuwa ko mun yi kuskure)) ya ce "Ya karba" to in Allah SW da aka saba masa ya yi wa mutum rangwame kai me zai sa ba za ka daga wa dan uwanka musulmi qafa ba? Akwai abubuwa 2 ga mutum in ya yi kuskure a malanta:
a) Mu da muka ji ba za mu bi shi a kan kuskuren ba, sai mu gyara masa.
b) Ba za mu rage masa komai ba abinda ya cancanta kamar jibanta, qauna da taimakawa, wannan shi ne matsaya ta qwarai da kowani musulmi ya kamata ya dauka tare da dan uwansa musulmi.
*GINSHIQI NA SHA TARA*
ADALCI
Wato ba wa mutane haqqoqinsu ba tare da an tauye musu komai ba, haqqoqi na abinda ake gani da wadanda kawai an san da su ne, akwai ayoyi da hadisai da dama da Allah SW yake mana fada kan mu yi adalci ya ce ((In za ku yi magana ku yi adalci koda ga makusantanku ne, ku cika alkawarin Allah, da wannan ya yi muka nasiya don ku wa'azittu. Al-An'am 152)).
Al-Baidawi na magana kan ayar da take cewa ((Kar ku bari mashedanta su hana ku yin adalci. Al-Ma'ida 8)) ya ce "Kar tsananin gabarku da mushrikai ya hana ku yi musu adalci, ku zo ku wuce gona da iri wurin
yin abinda bai halasta ba, (Tafsirin Baidawi aya ta 8) na ji wani raddi da za a yi wa wani malami sai da aka hankatso abinda ya yi yana matashi, wani kuma aka kamo aikin da ya fara yi na likitanci kafin ya koma fagen ilimi, wani aka ce soja ne ya saba zaman bariki shi ya sa ya fadi kaza da kaza, ina laifi a gyara kuskuren da ya yi kawai?
Zamuci gaba insha Allah.
*Gabatarwa: Abulfawzhaan*
*Follow my Facebook Page*
https://www.facebook.com/100625758324355?referrer=whatsapp
