WASU ABABEN LURA A YAYIN NAZARIN TARIHI 2


WASU ABABEN LURA A YAYIN NAZARIN TARIHI

Kabir Abubakar Asgar

Fitowa ta Biyu

A. TA’ASSUBANCI
Ta’assubanci dabi’a ce ta dan adam. Kowane mutum yana da wasu mutane da yake da alaqa da su. Kamar iyayensa ko surukansa ko malamansa ko ‘yan mazhabarsa ko siyasarsa ko mutanen gari ko yankinsu ko qabilarsu ko iyayen gidansa da makamantan haka daga cikin alaqoqin da ke sanya zuciyar mutum ta zama a shirye take da ta karbi abin da suke akai.

Abin da masana suka lura da shi a nan shine, wannan dabi’a ta son kai tana yin naso a cikin dukkan abin da mutane ke fadi ko suke rubutawa. In so samu ne kowa ya fi son tauraron wadanda yake qauna ya zamo a sama. Ya fi ganin gaskiya a cikin abin da suka yi ko suka fadi ko suka rubuta. Kuma zai yi iya yin sa ya cewa ya tabbatar musu da daraja ko ya kore musu naqasa.

Hatta malamai da marubuta da masu bincike, wadanda ake tsammanin su zamo suna da tsantsar adalci ba kowa ne a cikinsu ya tsira daga hakan ba. 

A cikin Tarikhul Islam, Zahabiy ya hakaito wata magana daga wani malamin tarihi mai suna Zaahiruddeen Al-Kazaruniy, a inda shi Al-Kazaruniy din ke magana akan tarihin shahararren sarkin Mongol din nan da ya karya dauloli dabam-dabam wato Hulagu Khan. Sanin kowa ne cewa Hulagu Khan qasurgumin mugu ne wanda ya ruqurguza garuruwa da dauloli kuma ya zubar da jini ba dan kadan ba. Amma da yake Al-Kazaruniy dan fadarsa ne wanda ke tare da shi a dukkan yaqe-yaqensa sai ya rubuta cewa: “Hulagu ya kasance mutum ne malamai da girmama su da kuma tausayin talakawansa”. Da Zahabiy ya kawo wannan magana sai ya ce: “Malamin tarihi idan ya zama dan fadar sarki adili ne sarkin nan ko azzalumi ko ma kafiri, to ba abin da zai iya illa fadi illa ya sharara qarya don kawai ya yaba wa mai gidansa”. 

Don haka ne masana kimiyyar tarihi ke cewa yana da muhimmanci wajen karanta tarihi, a kula da alaqar murubuci da mutanen da yake tarihinsu, musamman wanda alamu suka nuna yana da qarancin adalci kamar Al-Mas’udiy mai littafin Murujuz-Zahab.

(To be contined)
Post a Comment (0)