*ABUBUWA GUDA BIYAR (5) NA HABAKA HANKALI:*
1- Mayar da al’amura ga Allah kan duk abin da ya dame ka
2- Samar wa zuciya yaqiini wanda zai saukaka maka radadin kaddara mai daci
3- Qana’a da yalwar zuci: mai qana’a sai ka iske shi da cikar hankali ba za ka iske shi cikin kidimewa da daburcewa ba. Yana da girmama kai amma ba girman kai ba!
4- Sanin bambanci tsakanin masoyi da makiyi domin mu’amalantar kowane cikinsu bisa doron karantarwar Shari’ah.
5- Zaben abokiyar rayuwa(wato matar aure) bisa la’akari da iymaninta da kuma addininta kamar yanda Manzon tsira- sallal Laahu ‘alayhi wa sallam- ya koyar da mu.
Wadannan kadan ne daga cikinsu.
_Shaykh Muhammad Bin Uthman_
_[HafizahuL-Laah]_