JAWABIN BAYAN TATTAUNAWAR MALAMAI GAME MAHANGAR SHARI'A AKAN CUTAR CORONAVIRUS


*JAWABIN BAYAN TATTAUNAWAR MALAMAI GAME DA MAHANGAR SHARI’AH A KAN CUTAR CORONA VIRUS WANDA ULAMA FORUM ON COVID-19 YA SHIRYA TA HANYAR ZOOM DA WHATSAPP TSAKANIN RANAKUN RAMADHAN 21 - SHAWWAL 5, 1441H (MAY 14 - 28, 2020)*
Bismillahir Rahmānir Rahīm. Alhamdu lillah. Wassalātu was Salāmu alā Rasūlillah, wa Ālihi wa Ashābihi wa man wālāh.
*SHIMFIDA:*
ULAMA FORUM on COVID-19, wato Zauren Malamai a kan COVID-19 zaure ne da ya kunshi manyan malamai da daliban ilmi, da kwararrun ma’aikatan lafiya da masana daban-daban, da kuma wasu jagorori na Musulmi. An samar da shi ne tun bayan da ya tabbata cewa cutar Korona ta bayyana a Najeriya. A halin yanzu, ban da babban zaure mai mutane 25, akwai kuma zauruka biyu; daya na Malamai mai mambobi 45 da kuma na matasa ma su tasiri a social media mai mambobi 37.
Manufar samar da ULAMA FORUM on COVID-19 ita ce tuntubar juna, da tattaunawa da masana da bibiyar al’amura, da yin bincike mai zurfi domin gano mahangar Shari’ah da kuma ba da shawarwarin da suka dace ga dukkanin bangarorin al'umma game da mas’alolin addini da na zamantakewa tare da kokarin ganin an kiyaye tanade-tanaden Shari’ah a dukkanin matakan dakile yaduwar wannan annoba da kuma abubuwan da za su biyo bayan haka.
Baya ga tattaunawa da zaure ke yi a kullum, da bibiyar lamura a sassan kasar nan, zauren ya kan kallafa wa Malamai da masana daban-daban daga ciki da wajen kasar nan, yin bincike da gabatar da kasidu da jawabai game da hali da a ke ciki da kuma ba da shawara ga hukumomi da jagorori game da abubuwan da ke tasowa a wannan yanayi da a ke ciki.
Bayan zama tare da masana, da samun bayanai game da yanayin cutar Korona da halayyarta da matakan da kasashen duniya daban-daban suka dauka don yaki da ita da kuma darussan da Najeriya za ta koya daga gare su, zaure ya kallafa wa Prof. Ahmad Bello Dogarawa ya yi bincike mai zurfi a kan wasu mas’aloli na addini da ke da alaka da cutar Korona. Bayan ya kammala, an aika wa dukkanin Malamai da daliban ilmi da ke tare da wannan zaure domin dubawa da inganta bayanan.
*TATTAUNAWA TA MUSAMMAN A KAN MAS’ALOLIN KORONA:*
Ranar Alhamis 21 ga watan Ramadhan, 1441H (14.05.2020), zaure ya gabatar da zaman tattaunawa ta musamman bisa jagorancin Malam Aminu Inuwa Muhammad. A wannan zama, Dr. Bashir Aliyu Umar da Dr. Abubakar Muhammad Sani Birnin Kudu sun gabatar da bayanai, sannan Malamai da daliban ilmi da dama sun yi ta’alikoki da tambayoyi.
*ABUBUWAN LURA:*
A sakamakon tattaunawar da a ka yi, shugabanni da mambobin zaurukan sun yi lura da abubuwa da dama, wadanda suka hada da:
(1) Al’amarin cutar Korona ya shiga cikin abin da Malamai ke kira nazilah, wato wata sabuwar masa’ala ce a Shari’ah, da ke bukatar bincike da gano matsaya a kai, kuma ba lalle ne akwai kwatankwacinta a baya ba.
(2) Malamai magabata, musamman Malaman Mazhabar Malikiyyah, sun yi matukar kokari wajen tunkarar irin wadannan al’amura da fitar da matsayar Shari’ah a kai, musamman lokutan da a ka nemi shawararsu ko matsaya don sanin hukuncin Ubangiji a kai. Amma tunda mas’alar Korona magana ce da ke da alaka da kiwon lafiya, to lalle ne a koma ga amintattu daga cikin masana fannin kiwon lafiya wajen kimanta al’amura da daukar matsaya da ta dace da matsayin Shari’ah.
(3) Al’amarin cutar Korona ya zo da wani abu sabo wanda su kan su masana na lafiya da shugabanni sun shiga dimuwa kafin a fahimci irin dabi’ar cutar, har ya tilasta a ka rika kwan-gaba-kwan-baya, domin an dauki wasu matakai a kasashe da dama amma sai a ka ga illoli sun bayyana kuma a ka dawo a ka sake canzawa bisa yanda bincike ke kara haskawa. Don haka, ba abin mamaki ba ne a samu irin wannan daga bangaren Malamai ma su bincike a kan hukuncin Shari’ah.
(4) Akwai rubuce-rubuce da Malamai da masana da dama daga cikin Musulmi a duniya su ka fitar domin kusanto da fahimtar jama’a a kan wannan al’amari ko bayar da fatawa game da wasu mas’aloli da ke bukatar haka. Mu ma a nan yankin, akwai bincike da rubuce-rubucen da Prof. Ahmad Murtala na Jami’ar Bayero Kano da kuma Prof. Ahmad Bello Dogarawa na Jami’ar Ahmadu Bello Zaria su ka yi wadanda su ka kunshi muhimman bayanai kuma sun warkar da bukatar al’umma a mas’aloli da dama da ke da alaka da wannan cuta a mahanga ta Shari’ah.
(5) Akwai kwamitocin fatawa na kasa da kasa da kuma na kasashe daban-daban da majalisun Malamai da su ka yi nazari cikin lamarin Covid-19 da yadda matsalar cutar ta shafi wasu daga cikin al’amura na addini, kamar dakatar da sallar Jumu’ah, da sallolin farilla cikin jam’i, da sallar tarawihi/tahajjud a masallatai, da dakatar da sallar idi, da tafsirin Alkur’ani na watan Ramadhan a cikin jama’a masu yawa, da dawafi da umrah, da sauransu.
(6) A bangare daya, kwamitocin fatawa ko majalisun manyan Malamai na kasashen Saudi Arabia da Egypt da Kuwait da Iraq da Jordan da Mauritania da Morocco da Algeria da Palestine da UAE da Malaysia da Europe da North America da kuma da yawa daga daidaikun Malamai sun ba da fatawa game da halascin rufe masallatai da sauran wuraren da jama’a ke taruwa, na wucin gadi, don dakile yaduwar cutar, bisa la’akari da manyan manufofin Shari’ar Musulunci da kuma hukunce-hukuncen da suka shafi hali da yanayi na bukata (حاجة) da larura (ضرورة) da sauki (رخصة).
(7) A wannan kasa ta mu, kwamitin fatawa na Jama’atu Nasril Islam (JNI) da Nigerian Supreme Council for Islamic Affairs (NSCIA) da ke karkashin jagorancin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh ya yi nazari a kan mas’alar Covid-19 a mahangar Shari’ah kuma ya fitar da fatawar da ta tabbatar da halascin rufe masallatai na wucin gadi, da dakatar da sallar tarawihi da tafsirin Alkur’ani na watan Ramadhan a masallatai, da kuma yin sallar idi a gida.
(8) A daya bangaren kuma, kwamitin fatawa na Libya da kwamitin malaman Shari’ah da ke America da kuma daidaikun Malamai masu yawa daga kasashe daban-daban da wasu kwamitocin Malamai ma su zaman kansu, sun bayyana ra’ayoyi da su ka saba wa wadancan, kuma su ka yi fatawa da haramcin rufe dukkan masallatai na kasa baki daya bisa la’akari da matsayin masallatai a Musulunci, da hukuncin sallar Jumu’ah da sallolin farilla cikin jam’i, da kuma nasarar da a ke samu wajen yaki da cutar.
(9) Dukkanin mahalarta sun lura da irin gagarumar gudummuwa da manya da kananan mawadata da kuma kungiyoyin sa kai a sassan kasar nan su ka bayar wajen tallafa wa masu karamin karfi da abinci a lokacin dokar zaman gida (lockdown), da kuma taimaka wa gwamnatin tarayya da gwamnatocin jahohi da muhimman kayayyakin da a ke bukata don gudanar da gwajin tabbatar da cutar Korona da kuma inganta wuraren da a ke killace wadanda su ka kamu da ita.
*MATSAYA:*
Duba da abin da ya gabata, mahalarta tarurrukan da a ka yi duk sun gamsu da cewa:
(1) Cutar Korona wadda a ke kira da sunan Covid-19 wata sabuwar cuta ce fil, wadda ta fara bayyana a kasar China a karshen shekarar 2019. Don haka, ba bu wanda ke da cikakkiyar masaniya a kan ta, sai dai gwargwadon bincike da a ke yi a yanzu.
(2) Akwai Covid-19 a Najeriya, kuma cuta ce mai hadarin gaske don haka wajibi ne mahukunta su dauki matakan da suka dace don kare al’umma daga hadarinta. Haka kuma, wajibi ne mutane su bi shawarwarin amintattun kwararrun masana kiwon lafiya wajen kare kai da dakile yaduwarta cikin al’umma.
(3) Mas’alar Covid-19 na cikin Alqadhaya almasiriyyah, wato al’amuran da suka shafi makomar al’umma wadanda Allah SWT Ya sanya wuka da nama a hannun shugabanni domin daukar matsayar da za a dora al’umma a kai bayan sun yi shawara da amintattun kwararrun masana. Kuma, a karshe, matsayin da mahukuntan suka cinma, ko da wasu daga cikin masana ko Malamai su na da wani ra’ayin sabaninsa, shi ne ya wajaba kowa ya bi, kamar yadda aya ta 83 da ke suratun Nisa’i ta tabbatar. A cikin ayar, Allah SWT Ya ce: “Idan wani al’amari muhimmi ya zo musu, ko na aminci ko na tsoro, sai su yayata shi. Da sun mayar da shi zuwa ga Manzo da majibinta al’amari daga cikinsu, da masu zurfin bincikensa daga cikinsu za su san shi…”
(4) Kasancewar mas’alar ta zama ta ijtihadi, kuma kowane bangare ya dogara da dalilai na Shari’ah don tabbatar da manufofin Shari’ar Musulunci, hukuncin da shugabanni su ka yanke a kowace kasa ko jaha, shi ya wajaba mutanen kasar/jahar su bi, bisa ka’idar: التصرف على الرعية منوط بالمصلحة.
(5) Duk da sabanin fahimta ko ra’ayi game da mas’alar Korona, lalle ne a kaucewa tuhumar kowane bangare, ko yin batanci ko cin zarafin shugabanni da wadanda su ke tare da ra’ayinsu, ko kuma sauran malamai da su ka saba wa ra’ayin shugabanni wajen fatawoyinsu.
(6) Girmama shugabanni da yi ma su biyayya ya na daga cikin jiga-jigan turakun addinin Musulunci. Don haka, cin zarafi, da zagi da tuhumar imanin shugabanni tare da tunzura mabiya su ki yi ma su biyayya saboda sabanin fahimta, wannan ba daidai ba ne, kuma yin haka saba wa umarnin Manzon Allah SAW ne.
(7) Matakan kare kai da dakile yaduwar cutar, kamar sanya safar rufe baki da hanci, da yawaita wanke hannuwa da sabulu, da amfani da sanitizer, da nisantar wuraren da a ke cunkoso, da ba da ‘yar tazara a tsakanin mutane (social distancing) ko da a cikin sahun salla ne (a jahohin da a ka ba da damar haduwa a yi salla a masallatai), matakai ne da su ka dace da manufofin Shari’ar Musulunci game da kare rai. Don haka, akwai matukar muhimmanci a yi aiki da su.
(8) Dukkan mambobin zaurukan sun yarda da cewa akwai bukatar ci gaba da bibiyar al’amura, da yin nazarí cikin abubuwan da al’umma ke da tuhuma da zargi a kai wadanda su ka shafi siyasar duniya game da cutar Korona, kamar maganar asalin cutar Covid-19, da maganin rigakafin cutar da kuma alakarsa da shirin rage yawan al’umma, da kimiyyar 5G networks, da al’amuran da ke da alaka da tattalin arzikin kasashen Africa. Haka kuma, mambobi sun amince da ci gaba da tattaunawa da amintattun kwararrun masana kiwon lafiya da kuma tuntubar manyan Malamai na bangarori daban-daban da shugabbanin jama’a don samar wa al’umma mafita wadda ta dace.
(9) Akwai larurar samar da damar tuntubar juna a duk lokacin da irin wadannan mas’aloli na nazilah suka taso don a samu damar tattaunawa da daukar matsaya ta bai daya, maimakon kowa ya rika fadar fahimtarsa ba tare da la’akari da saukin yaduwar fatawowin ba.
*SHAWARWARI:*
Mahalarta tarurrukan sun tsayu a kan manyan shawarwari don samar da ci gaba da kuma bayar da gudummuwa don dakile wannan annoba kamar haka:
*SHAWARWARI GA HUKUMOMI*
(1) Shugabanni su rinka bibiyar canje-canje da a ke samu cikin lamarin Covid-19 tare da yin bitar tasirin matakan da a ke bi wajen yaki da cutar don fahimtar lokutan da ya dace a canza salo ko a yi garanbawul ga wasu dokoki, bisa la’akari da yanayin kasa da kuma halin jama’a.
(2) Duk abin da gwamnati za ta yi game da Covid-19 wanda zai shafi al’umma, ya kamata ta nemi shawarar Malamai game da matsayar addini, kamar yadda a ke neman shawarar likitoci da sauran masana.
(3) Hukuma ta saukaka hanyoyin da za su ba da damar a bi dokokin da ta ke sanyawa don dakile yaduwar cutar Korona.
(4) Horar da jami’an tsaro game da yanda za su nuna wa jama’a amfanin dokokin da a ka sanya masu, da kuma yanda za su lallashi mutane kan bin ka’idodin da hukuma ke sanyawa na da matukar muhimmanci.
(5) Hukumomi su bayar da dama ga Malamai da shugabannin al’umma a kafafen yada labarai don fadakarwa da wayar da kan jama’a game da cutar Korona, da muhimmancin matakan da a ke dauka don dakile yaduwarta. Gudummuwar Malamai da shugabannin al’umma a wannan bangaren za ta fi tasiri a kan jama’a fiye da ta wasunsu.
(6) Gwamnati ta fitar da sharudda masu karfi amma masu yiwuwa, wadanda galibinsu za a tabbatar da su kafin a bude masallatai (a jahohin da ba a riga an bude ba) don mika su ga kungiyoyi da kwamitocin masallatai, sannan a sanya lokaci na sa ido da kuma tabbatar da aiwatar da su.
(7) Shigar da kungiyoyi/jagororin Musulmi cikin aikin bibiyar tsarin tallafawa mabukata na gwamnati don sa ido da kuma shaida nasarori da matsalolin da a ke samu wajen aiwatar da tsarin.
(8) Hukumomi su samar da ingantaccen tsarin lockdown da zai takaita cunkoso a ranakun da a ke fita (a jahohin da ba a dage dokar ba).
(9) Yin shirye-shirye a radio da sauran kafafen da suka dace don fadakar da jama’a halin da a ke ciki, da nasarori da matsalolin da a ke fuskanta, tare da jinjina wa jama’a a kan hakuri da goyon baya da suke bayarwa ga matakan da a ke dauka. Wannan ya hada da shirya tattaunawa ta masana da Malamai don jama’a su saurari bayanai na likitanci da na Shari’ah, kuma a amsa tambayoyinsu a kan matakan da a ke dauka. Haka kuma, akwai bukatar hukumomi su nemi Malamai da masana kiwon lafiya su fitar da rubutattun bayanai, da clips na audio da video wadanda za su kunshi bayanai a kan janaza da binne mamaci a wannan lokacin ko da kuwa ba Covid-19 ce ta zama dalilin mutuwa ba.
*SHAWARWARI GA MALAMAI*
(1) Malamai su rinka nanata wa al’umma, shugabanni da mabiya, wajabcin komawa ga Allah, da kankan da kai gare Shi, da tuba, da istigfari, da yawaita sadaka da salati ga Manzon Allah SAW a matsayin mataki mafi muhimmanci wajen yaki da annobar Korona, ba tare da kore wajabcin riko da hanyoyin dakile ta ba.
(2) Malamai su kiyaye ka’idojin da hukuma ta kafa, tare da bin matakan kare kai a aikace, kuma su tabbatar iyalansu ma sun yi hakan gwargwadon iko don bayar da kyakkyawan misali ga jama’a.
(3) Ka da Malamai su rinka yin jawabai ma su tunzura mutane ko da da sunan fadar ra’ayi. Su yi amfani da minbarin Jumu’ah da sauran wuraren da suka dace don fahimtar da mutane game da cutar Korona da hanyoyin dakile yaduwarta bisa shawarwarin da amintattun kwararrun masana suka ba da.
(4) Duk abin da a ka ga ya dace hukuma ta yi, zai yi kyau Malamai su tuntubi juna don tattaunawa da jin shawarwarin juna, sannan a sanar da hukuma ta hanyar da ta dace, ba tare da fallasa ba a kan minbari ko majalisin karatu.
(5) Malamai da kwararrun masana kiwon lafiya su jagoranci samar da rubutaccen tsarin kariya a masallatan Jumu'ah kafin a kawo lokacin bude su da kuma bayan bude su, kamar cire carpets, da tsarin wanke tiles, da amfani da sanitizer, da sanya safar rufe baki da hanci (face mask), da sauransu.
(6) Malamai su yi kokarin fifita ijtihadi jama'i a kan fardi don gudun ka da a samu baraka a tsakaninsu ko kuma a jefa jama’a cikin rudani.
(7) Malamai su dage wajen nuna wa jama’a wajabcin biyayya ga shugabanni, musamman cikin mas’alolin da suka shafi al'umma a dunkule.
(8) A na tunatar da Malamai cewa hukunci a kan mas’ala yana ginuwa ne a kan kyakkyawar fahimtar wannan mas’ala (الحكم على الشيء فرع عن تصوره). Wannan ya nuna wajabcin zama da tattaunawa da kwarrarun masana kafin a zartar da hukunci ko fatawa ko bayani. Rashin yin haka ko takaitawa wajen yinsa tabbas zai ba yu ga kuskuren hukunci ko fatawa ko bayani.
(9) Kafin Malami ya bayar da fatawa a kan nazilah, ya yi la’akari da ruhin Shari’ah da manufofinta, kuma ya yi la’akari da tarihi, da canje-canjen da banbancin yanayi da hali da wuri da lokaci su ke kawowa.
(10) Malamai su ci gaba da fadakar da jama’a da yi ma su bayani game da muhimmancin ciyarwa da bayar da tallafi cikin al'umma, musamman a irin wannan lokaci da mafi yawan mutane ke fama da talauci da kuncin rayuwa.
(11) Wajibi ne tsoron Allah ya yi wa Malamai tasiri sosai wajen fuskantar al’amuran al’umma; ka da su fadi abubuwa cikin fushi ko hamasa, haka kuma ka da su rinka aibanta ‘yan uwansu Malamai saboda sabanin fahimta a cikin wannan mas'alar.
*SHAWARWARI GA JAMA’A*
(1) Jama’a su gamsu da cewa akwai cutar Korona, musamman da ya ke nagartattun amintattu kuma kwararrun masana sun tabbatar da ita a Najeriya da kasashe daban-daban na duniya.
(2) Duk da cewa ba za a kore yiwuwar tasirin siyasar duniya ba a cikin al’amarin Korona, ba daidai ba ne jama’a su rinka yin izgilanci ga matakan da a ke dauka don dakile yaduwar cutar ko kuma su yi biris game da hadarin da cutar za ta haifar idan ta yadu.
(3) Jama’a su daure su bi matakan kare kai, wadanda amintattun masana su ka nuna, kuma su yi hakuri da sababbin matakan da a ke dauka a masallatai da kasuwanni da sauran wuraren da jama’a da yawa ke haduwa, don ganin an samu nasarar dakile yaduwar cutar da iznin Allah.
(4) Masu hali da wadata cikin al’umma wajibi ne su taimaki talakawa da abin da za su ci, da kuma kyautar facemask domin a taimaka musu wajen bin dokokin da hukumomi su ka sanya.
(5) Jama’a su yi biyayya ga gwamnati kan wadannan matsaloli taré da fahimtar cewa a na daukar matakan ne don tunkude cuta da jawo amfani ga al’umma baki daya. Haka kuma, jama’a su nisanci aibanta shugabanni da kuma Malaman da suka nuna goyon baya ga matakan da hukumomi ke dauka wajen dakile yaduwar cutar.
*SAURAN SHAWARWARI*
(1) A na ba shugabanni da jagororin masallatai, musamman na Jumu’ah shawarar su samar da kyakkyawan tsarin tattara tallafi a ko yaushe a masallatansu don taimaka wa masu karamin karfi cikin jama’a musamman a lokacin da a ka shiga cikin hali na kuncin rayuwa.
(2) A na tunatar da ‘yan jarida wajabcin riko da ladubban aikin jarida wajen gudanar da ayyukansu; su daina ruwaito bayanan da ba su da sahihanci ko danganta magana ga wanda bai fade ta ba ko kuma ruwaito bayanan da za su gwara kan Malamai da shugabanni kuma su jawo rudani cikin al’umma.
Daga karshe, Zauren Malamai a kan COVID-19 na kara nanata wajabcin komawa ga Allah da kankan da kai gare Shi, da tuba, da yawaita istigfari da sadaka, da yawaita karatun Alkur’ani da salati ga Manzon Allah SAW, da addu’o’i, da kuma barin nau’o’in zunubai da sabon Allah. Haka kuma, Zauren na rokon Allah SWT Ya yaye wa al’umma wannan musiba ta cutar Korona kuma Ya ba mu ikon cin jarabawar da ke tattare da ita.
Alhamdu lillah. Wassalātu was Salāmu alā Rasūlillah.
SUNAYEN WADANDA SU KA HALARCI TATTAUNAWA
S/n Suna Jaha
01 Malam Aminu Inuwa Muhammad Kano
02 Dr. Bashir Aliyu Umar Kano
03 Prof. Mansur Ibrahim Sokoto Sokoto
04 Dr. Abubakar Muhamad Sani B/Kudu Jigawa
05 Dr. Khalid Abubakar Aliyu Kaduna
06 Prof. Muhammad Babangida Kano
07 Prof. Salisu Shehu Bauchi
08 Prof. Ahmad Bello Dogarawa Kaduna
09 Dr. Muhammad Alhaji Abubakar Borno
10 Malam Muhammad Lawal Maidoki Sokoto
11 Barr. Ibrahim Muhammad Attahir Gombe
12 Amir Abdullahi Abubakar Lamido Gombe
13 Dr. Abubakar Saidu Gombe
14 Dr. Salisu Ismail Sokoto
15 Engineer Ahmad Jumba Bauchi
16 Engineer Basheer Adamu Aliyu B/Kudu Kano
17 Malam Aminu Aliyu Gusau Zamfara
18 Sheikh Abdulwahab Abdallah Kano
19 Dr. Ibrahim Umar Adam Disina Bauchi
20 Prof. Ahmad Murtala Kano
21 Prof. Usman M. Shuaibu Zunnurain Kano
22 Dr. Muhammad Muslim Ibrahim Katsina
23 Dr. Rasheed Abdulganiy Gombe
24 Malam Shehu Muhammad Maishanu Zamfara
25 Dr. Abdallah Usman Gadon Kaya Kano
26 Sheikh Abubakar Abdussalam Gwale Kano
27 Dr. Rabiu Umar Rijiyar Lemo Kano
28 Dr. Saidu Ahmad Dukawa Kano
29 Dr. Muhammad Tanko Aliyu Nasarawa
30 Dr. Bashir Imam Aliyu Adamawa
31 Dr. Jamilu Yusuf Zarewa Kaduna
32 Dr. Ibrahim A. S. Rijiyar Lemo Kano
33 Sheikh Abdulmuttalib A. Muhammad Yobe
34 Malam Ahmad Bello Abu Maimoonah Katsina
35 Barr. Abdul’Aziz Abubakar Abdussalam Nasarawa
36 Sheikh Muhammad Bello Doma Gombe
37 Dr. Umar Garba Ibrahim Dokaji Gombe
38 Dr. Usman Ibrahim S. Giade Bauchi
39 Dr. Jabir Sani Maihula Sokoto
40 Dr. Mansur Isa Yelwa Bauchi
41 Dr. Abbdurrahman Idris Zakariyya Plateau
42 Prof. Auwal Magashi Kano
43 Dr. Magaji Falalu Zarewa Kano
44 Dr. Dahiru Inuwa Ibrahim Gombe
45 Dr. Usman Jibril Mika’il Gombe
46 Imam Abdul-Rahman Ibrahim Idris Bauchi
47 Sheikh Zakariyya Muazu Gombe Abuja
48 Sheikh Abba Muhammad Gadanya Kano
49 Sheikh Bashir Lawal Zaria Kaduna
50 Dr. Auwal Saad Tilde Bauchi
51 Dr. Ismail Ya’u Gombe
52 Sheikh Aliyu M. Said Gamawa Bauchi
53 Sheikh Haruna Doma Niger
54 Sheikh Yusuf Adam Khalil Kano
55 Dr. Abdulmuddalib A. Muhammad Kano
56 Sheikh Ibrahim Chiroma B/Kudu Jigawa
57 Sheikh Isa Garba Nayaya Yobe
58 Sheikh Adam Muhammad Ardo Gombe
59 Dr. Jameel Muhammad Sadis Kaduna
60 Sheikh Muhammad Sagir Usman Kano
61 Sheikh Muazu Abba Jabir Bauchi
62 Sheikh Musa Adam Maihula Gombe
63 Sheikh Idris Yunus Abuja
64 Sheikh Aminu Bala Kano
Post a Comment (0)