DAGA ZUCIYATA 01


DAGA ZUCIYATA 01

Da sunan Allah Rabba
Ba wa'azi zan yi muku ba 
Ba nasiha zan yi muku ba 
Ba damunku nake son yi ba 
Zance ne daga zuciyata zan furta. 

Damuwa ta aure ni 
Damuwa ta kama ni
Damuwa ta dame ni 
Damuwa ta kayar da ni 
Na bi duk na dagule a tunanin zuciyata. 

Ban san fa mai ya sa haka ba
Ban san fa mai na yi musu ba
Ban san yaya suke so ba
Ban san ya suke so na yi ba
Ban san menene yasa suke ƙina ba. 

Wai ni ba dogo ne ba
Wai ni ba siriri ba
Wai ni ai ban waye ba
Wai ni ban san komai ba
Wai shin sai yaushe ne za ku bar gaba?

So suke wai in yi kaza 
So suke wai in bar kaza 
So suke in je wuri kaza 
So suke in bar gu kaza 
So suke dai in zamo kamar banza. 

Sun ce min ɓarawon kaza 
Sun ce wai na saci reza 
Sun ce wai ai na yi kaza 
Sun ce wai ai nace kaza
Sun ce wai ni na zamo kamar geza. 

Saboda na ƙi zama wawa 
Saboda na gaza duƙawa
Saboda na gaza dainawa 
Saboda na gaza kasawa 
Saboda na zama wanda ya ƙi lalacewa. 

Shi ya sa basa sona 
Shi ya sa fa suke ƙina 
Shi ya sa suke tsorona 
Shi yasa suke ta guduna 
Shi ya sa suke min hassada a aikina. 

Ko da dai kun cuce ni
Ko da dai kun zalunce ni
Ko da dai kun tauye ni
Ko da dai kun fa tsane ni
Ko da ba kwa son gani na dai gani.

Zan ci gaba...

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 
Post a Comment (0)