HALASCIN MIJI YA NISHAƊANTU DA JIKIN MATARSA YAYIN DA TA KE HAILA

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_HALASCIN MIJI YANISHADANTU DA JIKINTANSA TANA HAILA KO NIFASI_* 

Akwai wani hali da miji yake shiga mai tsananin bukatuwa da mace idan matarsa tana cikin jinin haila ko jinin nifasi musamman ma idan ita ka dai ne a wajenshi.

To sai shari'a tace ya halatta ya umurce matarsa tayi kunzugu mai tsanani sannan ya kwanta da ita akan shimfida ya aikata duk abinda yaso da ita amma kada ya kuskura ya kwance kunzugun, kuma yana iya shafar ko ina a jikinta amma ban da iyakar cibiyarta zuwa gwiwarta, wannan bai halatta ba.

Kuma malamai sun ce ya halatta maigida ya fitar da maniyyi da hannun matarsa, amma bai halatta ya fitar da hannunsa ba.

An ruwaito ga Aisha (R.T.A) tace; "Annabi (S.A.W) ya kasance yana umurnina nayi kunzugu daga cibiya izuwa gwiwa, shi kuma yayi mubashara dani alhali ina cikin haila. Musline ya ruwaito

Wabillahi Taufia.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*

Post a Comment (0)