TAMBAYA TA 147


*KO ZAN IYA YIN WANKA IDAN JININ HAILA YA DAUKE KAFIN CIKAR KWANAKIN SA AMMA YA KOMA KALAR COFFEE !!*

*Tambaya*

Assalamu alaikum malam idan jinin haila ya dauke bayan Kwana biyar Amma Sai ana shida yake daukewa saboda kalarsa Yana zama coffee to ahaka zanyi wanka kokuwa Sai naga ya dauke duka naga fari tukunna kuma sannan idan naganshi har azahar to zanyi sallar axahar ne kokuwa la asar zanyi? 

*Amsa*

Wa'alaykumussalam
Idan jinin haila ya dauke kafin cikar adadin kwanakin sa, kuma duk alamomin daukewar sa ( farar kassa da bushewar gaba) duk sun bayyana toh babu laifi ayi wanka a ci gaba da ibada...
Amma idan kwanakin sa basu cika ba, kuma wadan cen alamomin biyu basu bayyana ba, toh baza'ayi wanka ba don anga wata alamar da ba wadancen biyun ba wato don ganin coffee/brown.

Wallahu A'alam
*Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)*

27 /05/2020

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

Ku Danna link din dake Qasa don kasancewa damu a shafin telegram👇
https://t.me/miftahul_ilmi

→Ga masu sha'awar shiga miftahul ilmi a WhatsApp sai su shiga ta nan su aika da cikakken suna 👇
https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)