SHAWARA GA MATAN AURE


SIRRIN MALLAKAN MIJINKI

Shawara Ga Matan Aure

Ya kamata duk matar da ta tsinci kanta a dakin aure a wannan zamanin da muke ciki yanzu, ta gode ma Allah. Ba don komai ba, idan ta duba za ta ga wasu ‘yan mata irin ta, sun fi ta kyawun halitta da iya ado, amma har yanzu ba su samu mijin aure ba.

Don haka zai fi alkairi a gareki ki kudurce a cikin zuciyarki cewa gidan mijinki nan ne wajen neman aljannarki, idan kika bi mijinki sauda kafa to za ki yi samun aljanna cikin sauki, idan kuma kika sabawa mijinki to ki sani za ki hadu da fushin Allah.

Ki rike mijinki hannu bibbiyu, ki kula da tsaftar jikinki da tsaftar muhallinku.
Kuma ki zama ko yaushe a shirye kike domin biyan bukatar mijinki ko da bai nema ba.
Ki kiyaye mugwayen kawaye wanda ba za su rasa yi miki hassada ba. Tunda ke kin samu miji su kuwa ba su samu ba dole su yi miki hassada. Don haka sai ki kula da irin sawarwari da za su iya baki.

Ki kiyaye sirrin mijinki, kar ki gaya ma kowa, musamman ma kawayenki za su so su ji abin da yake faruwa don haka kar ki gaya musu.

Idan kuna da ‘ya’ya to ki kula da su, ki kula da tsaftarsu idan ma ‘ya’yan kishiyarki ne, to ki kula da su kamar yadda za ki kula da ‘ya’yanki.

Ki kiyaye dukkan amanonin mijinki musamman ma iyayensa da ‘yan uwansa da dukiyarsa domin duka Allah zai tambaye ki.

Matan aure ku sani Aaljannarku yana tafin kafar mazajanku, idan kun yi masu biyayya to za ku samu aljanna cikin sauki. Allah ka sa maza da mata mu yi aiki da wannan shawarwari domin mu gudu tare kuma mu tsira tare.
 
Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: Abu Imam (Auwal Abdullahi)

Gabatarwa: Abu Imam (Auwal Abdullahi)

Zauren Macen Kwarai

Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.
Post a Comment (0)