TSAFTAR CIKIN ƊAKIN KWANA


*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Tsaftar Cikin Dakin Kwana:_* 

Dakin kwana dole ne mu kula da gyaranshi fiye da ko’ina a cikin gida, domin nanne wurin da Maidiga yake samun cikakken nutsuwa da hutawa da samun kwanciyar hankali da dai sauransu. Saboda haka dole ne mu riqa kula da gyaranshi qwarai da gaske, da kuma qoqarin qawatashi da duk abinda Allah ya hore, da qoqarin sanya turare da abubuwa masu sa qamshi a kowannen lokaci musamman lokacin kwanciya. In har Allah ya hore yana da kyau ayi amfani da turare na ruwa ko na hayaqi kala daban-daban, kina iya amfani da kala hudu ko biyar a lokaci daya kowannen ki sa shi a bangare daban. Misali na zanin gado daban, na filo daban, idan filon yafi daya kowanne ki sa masa nashi daban, na labule daban, na tsakar daki daban, na kujeru daban dss. Hakan zai bada wani irin qamshi mai tada hakalin Maigida ya rasa wanne irin qamshi ne wannan kuma daga ina yake fitowa !!!

Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*
Post a Comment (0)