WASU ABABEN LURA A YAYIN NAZARIN TARIHI 6


WASU ABABEN LURA A YAYIN NAZARIN TARIHI

Kabir Abubakar Asgar

Fitowa Ta Shida

E. ME YA SA BA MA DAUKAN IZINA DAGA TARIHI?

Sanin tarihin dan adam da al’ummomi da qabilu da qasashe da sanin tarihin ci gabansu da al’adunsu yana da tasiri wajen wayar da kan mutum da nuna mishi hanyar tsira da kuma yi masa wa’azi cikin nishadi.

Saboda wannan muhimmancin ne Alqur’ani mai girma ya kula kwarai da batun tarihin annabawa da al’ummominsu mabambamta da mutane iri-iri da qasashe dabam-dabam tare da bayyana sakamakon da Allah ya yi ga al’ummomin da suka kafirce. Kuma ya umurce mu da mu dau izina daga labaran kamar yadda kuma Allah (SWT) ya bayyana ga manzonsa cewa ya ba shi labaran ne don ya dakar masa da zuciya, don ya san cewa qaryatawar da kafiran Makka suka yi masa ba kansa farau ba.

Sai dai masana na jin takaicin cewa waqi’in abin da ke faruwa a cikin al’ummar dan adam yana nuni izuwa ga qarancin daukan izina daga tarihi. A wasu lokutan, galibin mutane suna gazawa daga cin moriyar hatta tarihin da faru a akan idonsu, ballantana akai ga wanda ya faru a wasu zamunna da suka shude.

Tambayar da har yau ake ta fafutukar sama wa amsa gamsasshiya ita ce: ‘Me ya sa ba ma daukan izina daga Tarihi’.

A qarqashin haka ne wani masani dan qasar Jamus yake cewa: “darasin da kadai muke dauka daga tarihi, shine ba ma daukan izina daga Tarihi”

(To be continued)
Post a Comment (0)