WANDA YA YI TSAYUWAR DARE


Wanda ya yi tsayuwar dare (Sallan dare) shi da matarsa Addu'ar Annabi (saw) zata same sa

عن أبي هريرة قال قال رسول الله صلى الله عليه وسلم رحم الله رجلاً قام من الليل فصلى وأيقظ امرأته فإن أبت نضح في وجهها الماء رحم الله امرأة قامت من الليل فصلت وأيقظت زوحها فإن أبى نصحت في وجهه الماء.

Daga Sahabi Abi Huraira (R) ya ce, Manzon Allah (saw) ya ce, Allah ya jik'an mutumin da ya tashi cikin dare, ya yi Sallah, kuma ya tashi matarshi, idan tak'i se ya yayyafa ruwa a fuskarta. Allah ya jik'an matar da ta tashi cikin dare zata yi Sallah, ta tashi mijinta idan yak'i se ta yi yayyafi ruwa akan fiskarsa.

Imam Abu Daawud ya ruwaito, kuma Albaniya ya ingantashi, Dariqus-salihin (61,pg)

Note:
•Ba 'karamin rashi bane ace magidanta basu ta6a yin aiki da wannan hadisi ba.
•Sannan ma'auratan da suke aiki da wannan hadisi zasu rik'a raya gidan su, da samun farin ciki da annushuwa.
•Sannan mata, idan mijin ki bai San wannan hadisi ba, kada kiyi saurin fara yayyafa mishi ruwa rana guda, a'a ku zauna cikin fahimta ki sanar mishi da wannan hadisi da irin Addu'a da Annabi (saw)ya yi ma wanda suka yi hakan. Ko da kin yi mishi hakan bazai zarge ki ba.se dai ma yaji dadi domin ya dace da macen kirki..

Allah Ta'ala ya bada ikon aikatawa
Post a Comment (0)