ADMINS KU JI TSORON ALLAH 2


*ADMINS KUJI TSORON ALLAH!!! 02*

*RADDI ZUWAGA MATA MASU SHIGA GROUPS DIN KOYAR DA JIMA'I*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*MAJALIS - SUNNAH*
.
.
مجلس السنة
📓📔
+2349032091131
+237665087032
.
.
Yau 16/ 11/ 1441 wanda yayi dai-dai da 07/ 07/ 2020.
=
=
_Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa, muna neman taimakonsa, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyuakanmu. Hakika Wanda Allah ya shiryar Babu Mai 6atar dashi, Wanda ya 6atar Kuma Babu mai shiryar dashi. Kuma Ina Shaidawa babu abinda bautawa da Gaskiya sai Allah shi kadai, kuma ba shi da abokin tarayya. Kuma Ina Shaidawa Muhammad bawansa ne Kuma manzonsa ne._

_Bayan haka, jama'a idan kuna tare damu munyi bayani gameda ainihin admin da kadan daga cikin sharrinsu. Yau kuma insha Allah zanyi bayani gameda mata masu shiga groups wanda ba Allah da Annabi ake koyarwa ba aciki insha Allah._

_Yan uwana mata yakamata ku cigaba da kame kawunanku ta hanyar kame mutuncinku da na iyayanku daga sharrukan zamani, kada ku yarda rudun duniya yasa ku kauce daga tarbiyyan da aka ginaku akai, tabbas iyaye na kokari wajan kula da tarbiyyanku da mu'amalarku ta hanyar sa idanu akanku, tho idan kun fahimci wannan da kyau, ashe yakamata kuyi kokari wajan cigaba da kare kanku ta hanyar nisantar abinda Allah ya hana ko kuma abinda ya saba ma al'adarmu, kada ku dinga ganin fashion ya shigo gari kema kice bari ki shiga fashion a dama da ke. Babu shakka yin hakan kuskure ne wasu matan suka debo abinda wasu matan kasashe ke yi, ku kuma ku mayar dashi abin burgewa ko kuma ku kamashi ku rike har ma ku dinga yi fiye da yadda su sukeyi. Ku cigaba da yima iyayanku biyayya, ku cigaba da yiwa mijinku biyayya, ku cigaba da tsare mutuncinsu da naku, domin kana ganin yarinya ta gari, kasan daga gidan mutunci ta fito, amma in kaga mara tarbiyya, tho ba sai an fada maka kasan daga inda ta fito._

_Abu na farko da zan fada muku shine, Dan Allah, dan girman Allah, idan kinsan kina cikin group kamar haka;- *MATSALOLIN JIMA'I, RAYUWAR JIMA'I, MA'AURATA, ZUMUNCI, SOYAYYAH, SIRRIN RIKE MACE KO MIJI, MASOYI GROUP,* da dai ire-ire irin wadannan groups din, tho kiji tsoron Allah ki fita daga cikinsu tsaf, idan ba haka ba tho zaki shiga bala'i ranar tashin alkiyama, zaki shiga masifar da admin bazai iya miki komai ba, za a saki a wuta kina ganin admin zai taimake ki ya dinga miki gwalo musamman idan ya tuba anan duniyar. Wallahi kada kiyi girman kai ki qi fita, kada ki bari shaidan ya rudaki ki qi fita daga ciki. Idan Allah yasa kika kasance cikin wadanda suka karanta wannan sakon, amma kika qi tuba ki fita daga cikin groups din, tho wallahi bakida hujjar da zaki gayawa Allah ranar tashi alkiyama._

_Ranar alqiyama Allah zai ce:- *"YAKU TAWAGAR ALJANU DA MUTANE, SHIN MANZANNI DAGA CIKINKU BASU ZO MUKU BANE? WADANDA SUKE BAKU LABARIN AYOYINA NA ALQUR'ANI DA AYOYI NA RAYUWA, KUMA WADANNAN MANZANNIN NAKU HAR SUNA MUKU GARGADIN WANNAN YININ NAKU NA CEWA ZAKU HADU DA KIYAMA"* Jama'a mun fahimci wannan ayar da kyau? Tho idan kun fahimta da kyau zaku gane a ranar tashin alkiyama Allah zai yiwa aljani da mutane wannan tambayar. Sannan Allah ya sake cewa:- *YAKU TAWAGAR ALJANU DA MUTANE, IDAN HAR ZAKU IYA KUBUCEWA TA WANI KURDI NA SAMA KO TA KASA, SAI KU KUBUCE MU GANI. BAZAKU IYA KUBUCEWA DAGA WANNAN DANDALI BA SAI KUNADA WATA HUJJA"* Jama'a ita kuma wannan ayar tana maganar in aka taru a dandalin alkiyama, kamar yadda hadisi ya fassarata karara, acikin hadisin Bukhari, Manzon Allah s.a.w yace: "In aka taru a dandalin alkiyama, Allah madaukakin sarki da kanshi zai zo tareda Mala'iku, kamar yadda yace: *"UBANGIJINKA ZAI ZO DA MALA'IKU SAHU-SAHU"*. Wato Mala'iku zasuyi sahu suyi round kamar yadda ake kewaye dakin Allah a makkah, suma Mala'ikun zasu kewaye su, aljanu da mutane an zuba su a tsakiya sannan ga Allah madaukakin sarki kuma zaiyi hukunci da kanshi. Tho a wannan lokacin kunga Allah yana wurin a wannan sahu-sahun, shine sai Allah yace:- *"YAKU ALJANU DA MUTANE WANNAN RITSA KUN DA AKAYI, WANDA DUK ZAI IYA GUDU YA GUDU MU GANI"* Kafin na cigaba inaso tun anan duniya ku gudu daga groups din gaba daya, idan kukaje wannan taron wallahi bazaki iya gudu ba, ashe dolene ki shiga wuta. Tho sai Allah madaukakin sarki da kansa yace:- *"AMMA BA WANDA ZAI IYA KUBUCEWA YA GUDU DAGA NAN, SAI IN YANA DA WATA HUJJA SHINE ZAI TAFI WUTA KO ALJANNAH"* Tho jama'a ina ma'anar su tafi wuta? Shine yanada hujja akan kafircin da yayi? Tanada hujja akan groups na iskancin da kika shiga? Kinada hujja akan turawa wani gardi hotunanki a tsirara? Tho tunda batada hujja kuwa kuwa wuta zata tafi. Kunji dalilin da zai sa ki bar wannan wurin. Ina fatar kungane wannan da kyau?? Tho wane yanada hujja da yayi tauheedi? Yanada hujja da ya shiga groups din da ake koyar da kitabu-was-sunnah? Eh yanada hujja. Tho kunji dalilin da zai rabashi ya tafi aljannah. Inba kanada hujja ba, tho bazaka bar wannan gurin ba, kuma idan ka tashi barin wannan gurin, tho ko dai kaje aljannah ko kuma kaje wuta._ 

_A karkashin haka nace wallahi bakida hujjar da zaki fadawa Allah kina turawa wani kato ko wata gardiya hotunanki a tsirara. Na rantse da Allah bakida hujja, saboda haka wallahi wuta zaki tafi, saboda haka ki tuba ki fita daga duk wani group din da kikeci a yanzu matukar ba Allah da Annabi suke koyarwa ba. Tho wallahi ku fita ku tuba, tun kafin lokacin ya kuremiki._

_Saboda haka kusani masu bude ire-iren wadannan groups din, tho shaidanu ne daga cikin mutane, shiyasa irinsu basa tuba da wuri, kuma zan fada muku wani labarin yadda sukeyi acikin group din a lekca ta gaba insha Allah. Shin kinyi alkawari idan kika karanta wannan bayanin zaki tuba ga Allah? Kin yarda cewa bakida hujjar da zaki fadawa Allah ranar tashin alkiyama? Idan kin yarda kika tuba, tho anan ma sai ki tambaya yaya zakiyi ki tuba kuma Allah ya karba, saboda haka sai kuje ku tambaya._

_Ya Allah muna rokonka ka ba iyayenmu mata ikon rike mutuncinsu har gidan mazajensu, kasa su rabu da iyayansu suna masu farinciki dasu, ka tsaremu, ka tsare zuri'o'inmu daga dukkan sharrin zamani, ya Allah ka kare mana su daga dukkan abin qi. Allah ta'ala ya taimake mu._
=
=
_Dan uwanku a musulunci_
°
*_✍Abdulrasheed Ibn Musa Abms_*
°
°
.
Allah ta'ala yasa mudace
.
.
https://www.facebook.com/Zauren-Majalis-Sunnah-420869088334488/?referrer=whatsapp
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
Post a Comment (0)